EndSARS: Na ja hankalin mutane a kan lamarin COVID-19, aka ki ji inji Yahaya Bello

EndSARS: Na ja hankalin mutane a kan lamarin COVID-19, aka ki ji inji Yahaya Bello

- Yahaya Bello ya bugi kirji, ya ce akwai siyasa a zanga-zangar #EndSARS

- Gwamnan ya bayyana abin da ya jawo wasu su ka rika satar kayan tallafi

- Bello ya ce Jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa sun samu riba da COVID-19

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi hira da gidan talabijin na Channels TV inda aka yi magana da shi game da zanga-zangar #EndSARS.

A ra’ayin gwamna Yahaya Bello, zanga-zangar #EndSARS ta na da burbushin siyasar 2023.

Ya ce: “‘Yan Najeriya, bari in fada maku wannan, zanga-zangar EndSARS ta na da burbushin siyasa. Ko wani ya fada, ko bai fada ba, ni na fada.”

KU KARANTA: Masu neman satar kayan tallafi sun ga dakin adana wayam a Bauchi

“Me zai sa ku kawo bukatu biyar, kuma a amince da su, sannan ku ki karba? Wace gwagwarmaya aka taba yi a Duniya aka ci nasara babu shugaba?"

Gwamna Bello ya ce tun farkon shigowar COVID-19, ya ja-kunnen jama’a, amma aka yi masa kunnen-shegu, a karshe wasu su ka yi kudi da annobar.

Gwamnan ya ce wadanda su ka saci kudi da dukiyar al’umma da sunan annobar, wasu ‘yan Najeriya ne da ke ciki da wajen gwamnati da ‘yan kasuwa.

A cewar gwamnan, Kogi ce kadai Jihar da ta ki yarda akwai cutar COVID-19 da za ta kashe jama’a.

KU KARANTA: A karshe, Matasa sun gano gaskiyar Ministar bada tallafi

EndSARS: Na ja hankalin mutane a kan lamarin COVID-19, aka ki ji inji Yahaya Bello
Gwamna Yahaya Bello Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Game da tallafin COVID-19 da aka raba, gwamnan ya ce ya guje wa gudumuwar N1.1bn daga bankin Duniya, don haka bai karbi kayan Ca-COVID ba.

Gwamnan ya ce: “Masana sun ce za a shiga rikici; an rufe matasa a gida, ASUU ta na yajin-aiki, ana samun yawan laifi, sai matasa su ka gano kayan tallafi.

A karshen makon jiya aka ji cewa wasu tsageru sun labe da zanga-zangar #EndSARS da ake yi, sun je sun kai hari a ofishin Jam’iyyar APC a jihar Delta.

Bata-garin sun shige cikin rigar zanga-zangar #EndSARS, sun jawo wa jam'iyyar APC asara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng