Al'umma su ka hana wasu ‘Yan iska da aka yi haya kona mani gida – Dino Melaye

Al'umma su ka hana wasu ‘Yan iska da aka yi haya kona mani gida – Dino Melaye

- Dino Melaye ya ce an yi hayar ‘Yan daba su kona gidansa a Aiyetoro-Gbede

- Tsohon Sanatan ya ce matasa da mata su ka taru a gidan, su ka hana a kona

- Melaye ya zargi wani ‘dan siyasa da bai bayyana sunansa ba da wannan aiki

Dino Melaye wanda ya wakilci Kogi ta yamma a majalisar dattawa, ya ce mutane sun tsaya masa a lokacin da aka nemi a kona masa gida.

Sanata Dino Melaye ya ce an dauko wasu ‘yan iskan gari domin su kona gidansa da ke kauyen Aiyetoro-Gbede, amma ba ayi nasara ba.

Melaye ya bayyana haka ga jaridar Punch a lokacin da aka tuntube shi a wayar tarho a ranar Talata.

KU KARANTA: Wacece Dame Jonathan, ina ta yi karatu? ina aka haife ta? A ina ta yi aiki?

Tsohon ‘dan majalisar ya ce jama’a rututu musamman matasa sun taru, sun tare a gidansa, da su ka fahimci ta’adin da ake kokarin ayi masa.

Sanata Melaye ya ce an hangi wadannan tsageru ne cikin motoci 15 a kan titi dauke da makamai.

“Mutane na sun shiga cikin gidana a lokacin da su ka samu labarin sharrin da ‘yan-iskan garin su ka yi tanadi, su ka tsare gidan nawa.” Inji shi.

Ya fada wa ‘yan jaridar: “Miyagun sun koma da su ka ji cewa mutanena sun shirya masu.”

KU KARANTA: Martanin da Sanata Shehu Sani ya yi wa Macron kan yi wa Musulunci batanci

Jama’a su ka hana wasu ‘Yan iska da aka yi haya kona mani gida – Dino Melaye
Dino Melaye Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Melaye ya rubuta a Twitter: “Kokarin al’ummar gari ya hana tsageru kai wa gidana hari a Aiyetoro Gbede, na gode wa matasan Okun da matansu.”

Ya ce: “Jami’an tsaro sun yi kokari su ma. Fiye da komai, na gode wa Allah madaukakin Sarki.”

“Burinsu shi ne su ruguza gidan.”

Fitaccen Lauyan nan, Femi Falana ya fallasa wadanda su ka harbi masu zanga-zangar #EndSARS a Legas, ya ce aikin jami'an sojoji ne ba kowa ba.

Falana ya ce sun gano inda sojojin da su ka yi harbin su ka fito, amma bai fadi sunan barikin ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel