Siyasar Najeriya
Za ku ji wasu Gwamnonin da su ka yi tazarce bayan sun fice daga APC zuwa PDP. Godwin Obaseki ya kafa tarihin lashe zabe sau biyu a jere a Jam’iyyu dabam-bam.
Zababben gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya jaddada cewa ba zai bar jam’iyyar PDP wacce ta bashi damar lashe zabe ba zuwa ta APC wacce ta hana shi takara.
Gwamna Godwin Obaseki ya yi jinjina ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan zaben gwamnan Edo, ya bayyana cewa ya yi nasarar lashe zaben ne saboda adalcinsa.
Jiya Rabiu Kwankwaso ya yi magana bayan Jam’iyyar PDP ta lashe zaben Jihar Edo. Tsohon Gwamnan ya ce barazanar wasu kasashen waje sun taimaka wajen nasarar PDP.
Wani daga cikin manyan APC, ya yi magana game da zaben Gwamnan Jihar Edo. ‘Dan siyasar ya ce al’ummar Edo sun ki zaben APC ne saboda tsoma bakin wasu manya.
A jiya ne APC ta watsawa ‘Dan takararta kasa a ido, ta ce babu alfasha a zaben Edo. An kammala zabe PDP ta yi nasara, amma Osagie Ize-Iyamu ya ce an yi magudi.
Wasu ‘Ya ‘yan APC a Ekiti sun ce Dr. Kayode Fayemi ya goyi bayan takarar Godwin Obaseki. Obaseki ya doke ‘Dan takarar APC Osagie Ize-Iyamu a zaben makon jiya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, ya karbi bakuncin Gwamna Mai Mala Buni da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a fadar Villa.
Kamar dai a zaben 2016, Ize Iyamu ya gaza doke Godwin Obaseki duk da ya koma tafiyar jam’iyyar APC. Sau 2 kenan ‘Dan siyasar ya na rasa zabe a cikin shekara 4.
Siyasar Najeriya
Samu kari