Fitaccen Jarumin Kannywood Ya Fice Daga Tafiyar Rarara Ta Goyon bayan Tinubu
- Fitaccen jarumin Kannywood, Rabiu Rikadawa, ya sanar da ficewarsa daga ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope
- Rikadawa ya bayyana matakin ne a ranar Juma'a, 3 ga watan Yulin 2026, yana tabbatar da cewa ya fice daga tafiyar
- Jarumin ya ce ya fice daga ƙungiyar da mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ke jagoranta, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tafiyar goyon bayan shugaban kasa, Bola Tinubu daga bangaren yan masana'antar Kannywood ta fara samun matsala.
Fitaccen jarumi kuma dattijo a masana'antar, Rabiu Rikadawa ya fice daga tafiyar 'Triple R Kannywood' a Najeriya.

Source: Facebook
Dan wasan Kannywood da ya shafe shekaru a masana'antar ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a yau Juma'a 3 ga watan Yulin 2026.
Rikadawa ya fice daga tafiyar Rarara
Ya tabbatar da cewa ya fice daga tafiyar wacce mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ke jagoranta.
Jarumin ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan rashin gamsuwa da tsarin da ake yi a cikin tafiyar.
Rikadawa ya rubuta cewa:
"Ni Rabiu Rikadawa na fita daga wannan kungiya ta 'TRIPLE "R" KANNYWOOD FOR RENEWED HOPE' a yau 3 ga watan Yulin 2026 kuma a yanzu karfe 8:30 na safe."

Source: Facebook
Dalilin ficewar Rikadawa daga tafiyar Rarara
Dan wasan Kannywood ya bayyana cewa ba a yi masa adalci ba game da gudunmawar da ya bayar a tafiyar da ake yi.
Rikadawa ya bayyana haka ne a wani hira da ya yi da shafin DCL Hausa wanda aka wallafa a Facebook.
Dattijon ya ce tun farkon tafiyar an tabbatar da cewa mutum idan ya shiga wannan tafiya bai isa ya tallata kowa ba sai dan takarar APC a fadin Najeriya.
Ya ce:
"An ce mana za a yi tafiyar don ci gaban masana'anta da kuma kasa baki daya, mun je Abuja da kuma Gombe, sannan kuma an ce mana idan muna ciki ba za mu yi ba har sai yan takarar APC, an ce duk kyawun dan takara idan ba dan APC ba, ba za ka yi shi ba"
Rikadawa ya karyata rahoton cewa an kore shi ne daga tafiyar inda ya ce kwata-kwata hakan ba gaskiya be ne kuma jita-jita ce marar tushe.
Wannan ba shi ne karon farko ba da jaruman Kannywood ke ficewa daga tafiyar, a yau ma Ramadan Booth ya bayyana a Facebook cewa ya fita daga tafiyar da aka kirkira domin Tinubu da APC.
Hisbah ta magantu kan aurar da Nafisa
A wani labarin, an ji cewa majiyoyi sun nuna cewa hukumar Hisbah ta Kano ta buƙaci wani mai hannu da shuni ya nemi auren jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi.
Mataimakin babban kwamandan Hisbah, Dr Mujahid Aminuddeen, ya ce hakan zai zama babbar gudunmuwa ga addinin Musulunci.
Ya ce maimakon zagi da cin mutuncin fitattun mata da ke yin irin waɗannan kalamai, ya kamata a taimaka musu ta hanyar aurensu.
Asali: Legit.ng


