Majalisa Na Neman Taka wa Tinubu Birki kan Tubabbun Yan Ta’adda a Najeriya

Majalisa Na Neman Taka wa Tinubu Birki kan Tubabbun Yan Ta’adda a Najeriya

  • Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin Tinubu ta dakatar da shirin gyaran tubabbun 'yan Boko Haram da yan ta'adda
  • Sanatoci sun bayyana cewa kashe Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya bayan sace shi ya nuna tabarbarewar tsaro
  • Rahotanni sun nuna Borno ta kashe kusan Naira biliyan 7.7 wajen gyarawa da dawo da tubabbun 'yan Boko Haram

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta ba gwamnatin tarayya hawara game da shirin gyaran tarbiyyar tubabbun yan ta'adda.

Majalisar ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ta dakatar da shirin gyarawa da dawo da tubabbun 'yan Boko Haram cikin al'umma.

Majalisa ta tura bukata ga Tinubu kan rashin tsaro
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: The Nigerian Senate, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Majalisa ta fusata kan rashin tsaro

Sanatocin sun ce ci gaba da kashe-kashe da sace mutane, musamman jami'an soja masu aiki da masu ritaya, ya nuna cewa lokaci ya yi da za a sake duba wannan tsari, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Rahoton WFP: ADC ta zargi Tinubu da jefa miliyoyin mutane cikin yunwa a jihohin Arewa 9

An cimma wannan matsaya ne bayan amincewa da wata ƙarin bukata a zaman majalisar, yayin da sanatoci ke tattauna matsalar rashin tsaro da ke kara ta'azzara a sassa daban-daban na ƙasar.

Sanata Joseph Ikpea mai wakiltar Edo ta Tsakiya ne ya gabatar da ƙarin bukatar, kuma aka amince da ita ta hanyar kuri'ar murya lokacin nazarin kudirin da ya shafi hare-hare, garkuwa da mutane da kashe jami'an soja masu aiki da masu ritaya.

Sanata Abdulaziz Yar'Adua mai wakiltar Katsina ta Tsakiya kuma shugaban kwamitin majalisar kan rundunar sojin ƙasa ne ya dauki nauyin kudirin.

An dauki wannan mataki ne bayan sace tsohon Daraktan Yaɗa Labaran Tsaro, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda daga baya ya rasu yana hannun masu garkuwa da mutane bayan an sace shi tare da matarsa a Katsina.

Sanatoci sun bayyana cewa mutuwar Janar Abubakar wata babbar alama ce da ke nuna yadda matsalar rashin tsaro ke kara muni a Najeriya.

Ana yaye tubabbun yan ta'adda a Borno
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno da ke fama da ta'addanci. Hoto: Professor Babagana Umara Zulum.
Source: Original

Tubabbun yan ta'adda: Martanin Sanata Oshiomhole

Sanata Adams Oshiomhole ya goyi bayan dakatar da shirin gyaran tubabbun 'yan ta'adda, yana cewa bai dace a rika ba masu laifi lada ta hanyar yafiya da gyaransu ba.

Kara karanta wannan

Ma'aikata sun gabatar da sabon mafi ƙarancin albashin da suke buƙata a Najeriya

A cewarsa, babu wata hujja ta hankali da za ta tabbatar da bai wa masu aikata laifi afuwa tare da gyara su maimakon hukunta su.

Yayin muhawarar, Sanata Yar'Adua ya bayyana matsalar tsaro a matsayin gaggawar ƙasa, cewar Sahara Reporters.

Har ila yau, ya kara da cewa mutuwar Janar Abubakar da sauran wadanda suka mutu a hannun 'yan ta'adda babban rashi ne ga kasa, kuma gargadi ne kan girman matsalar tsaron da ake fuskanta.

Gumi ya nema wa yan bindiga afuwa

Mun ji cewa Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci Gwamnatin tarayya ta yi wa ‘yan bindiga afuwa kamar yadda aka yi wa tsofaffin mayaƙan Boko Haram.

Malamin ya ce amfani da ƙarfin soji kaɗai bai kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta shafe akalla shekaru 17 ana addabar jama'a da kashe rayuka.

Sheikh Ahmad Gumi ya musanta zarge-zargen cewa yana goyon bayan ta’addanci ko ayyukan ‘yan bindiga da ke addabar talakawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.