'Ka Tuna Kamfen da Muka Yi Maka a Baya': Matar El Rufai Ta Roki Tinubu
- Matar tsohon gwamnan Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta roƙi Shugaba Tinubu game da halin da mijinta ke ciki
- Asia ta ce sun yi wa Tinubu kamfen sosai a zaɓen 2023, tana jaddada cewa ba sa neman tsoma baki, sai dai a ba El-Rufai beli mai sauƙi
- Iyalan El-Rufai sun zargi ana hana shi ganin likitocinsa, lauyoyinsa da 'yan uwansa, yayin da ICPC ke zargin ya karya sharuɗɗa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Matar tsohon gwamnan Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai ta roƙi Shugaba Bola Tinubu kan halin da Nasir El-Rufai ke ciki.
Asia ta bukaci Tinubu ya tabbatar mijinta ya samu adalci da haƙƙoƙin da kundin tsarin mulki ya tanada.

Source: Twitter
Rokon da matar El-Rufai ta yi wa Tinubu
Asia ta yi wannan kira tare da matar El-Rufai ta biyu, Aichatou, a Abuja, tana mai cewa ba sa neman shugaban ƙasa ya tsoma baki, cewar Punch.
Ta ce suna so kawai a bai wa tsohon gwamnan damar cin gajiyar haƙƙoƙin da doka ta bai wa duk wani ɗan Najeriya.
Asia ta kuma yi zargin cewa mijinta na fama da hawan jini da ciwon sukari, amma ana hana shi samun kulawar lafiya yadda ya kamata.
Ta tunatar da irin rawar da ita da mijinta suka taka wajen yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ta ce:
"Ya kai Shugaba Tinubu, na yi maka kamfen a ko'ina cikin Kaduna, mijina ya tsaya tare da kai. Shin wannan ne sakamakon?"

Source: UGC
Iyalan El-Rufai sun yaba halin Tinubu
Asia ta ce komai na iya sauyawa idan Shugaba Bola Tinubu ya ɗauki mataki, tana mai bayyana cewa suna ganin shugaban mutum ne mai tausayi.
Ta jaddada cewa ba sa neman a dakatar da shari'ar El-Rufai, amma suna son a mutunta haƙƙoƙinsa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Ta ce a ba shi beli mai sauƙin cikawa, sannan kotu ta yanke hukunci idan an same shi da laifi ko kuma aka wanke shi.

Kara karanta wannan
Kaduna: Ana zargin an nadi muryar Isa Ashiru yana caccakar El Rufai a wayar tarho
Asia ta yi zargin cewa ci gaba da tsare El-Rufai da hana shi ganin likitoci, lauyoyi da 'yan uwansa ya jefa iyalansu cikin tashin hankali.
Ta ce kullum suna rayuwa cikin fargabar samun mummunan labari, tana mai cewa abin da ake yi musu tamkar yaƙin ƙwaƙwalwa ne.
Iyalan sun ce ana hana El-Rufai damar ganin likitocinsa na kai tsaye, yayin da ziyarar 'yan uwa ta ƙara zama mai wahala, cewar Tribune.
Sun kuma nuna shakku kan rahoton lafiya da aka danganta da Asibitin Ƙasa da ke Abuja, suna neman a binciki sahihancinsa.
ICPC ta cafke likitan El-Rufai
An ji cewa hukumar ICPC ta zargi tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da karya sharuddan ziyarar asibiti da kotu ta amince masa yayin da yake tsare.
Hukumar ta kuma kama likitan El-Rufai Farfesa Bello Abubakar bisa zargin bayar da bayanan karya yayin gudanar da binciken da ake yi.
ICPC, mai binciken cin hanci da rashawa ta ce za ta sanar da kotu yadda aka yi amfani da damar ziyarar asibiti ba bisa manufar umarnin kotun ba.
Asali: Legit.ng
