2023: Wasu manyan jiga-jigan PDP 3 sun sake sauya sheka zuwa APC

2023: Wasu manyan jiga-jigan PDP 3 sun sake sauya sheka zuwa APC

  • Jam'iyyar PDP a jihar Kuros Riba ta gamu da babban koma baya yayin da manyan jiga-jiganta uku suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
  • An bayyana hakan ne a wani babban taron masu ruwa da tsaki wanda Gwamna Ben Ayade ya jagoranta, a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, a Peregrino a jihar
  • Rahoton ya nuna cewa tsoffin jiga-jigai uku da ke da alhakin nasarar da PDP ta samu daga 1999 zuwa 2015 yanzu sun zama ‘yan PDP

Kuros Riba - Rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar adawa ba ta dauko hanyar karewa ba yayin da tsoffin shugabanninta uku na jihar, wadanda ake ganin sune ke da alhakin nasarar PDP daga 1999 zuwa 2015, suka koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Allah ne ya haɗa mu: Kwankwaso ya magantu kan haɗuwar shi da Ganduje

Jaridar Leadership ta rahoto cewa 'yan siyasar uku wanda suka yi aiki tare da tsoffin gwamnoni biyu a jihar, yanzu sun zama yan jam'iyya mai mulki.

2023: Wasu manyan jiga-jigan PDP 3 sun sake sauya sheka zuwa APC
Tsoffin shugabannin PDP uku sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kuros Riba Hoto: Sir Benedict Ayade
Asali: Facebook

Sauyin shekar gwamnan jihar Kuros Riba, Sanata Ben Ayade zuwa jam'iyyar APC a 'yan watannin da suka gabata, ya yi babbar illa ga tsohuwar jam'iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Yayin da Ambasada Soni Abang ya yi aiki a lokacin Gwamna Donald Duke, Ntufam Ekpo Okon da Ntufam John Achot Okon duk sun yi aiki a lokuta daban-daban a karkashin Gwamna Liyel Imoke.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton Vanguard ya nuna cewa tsoffin shuwagabannin sun daidaita kansu da hangen Gwamna, Farfesa Ben Ayade, wanda shine shugaban jam'iyyar a jihar.

Da yake magana a wani taron masu ruwa da tsaki wanda Gwamna Ayade ya jagoranta a Peregrino a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, Soni Abang ya bayyana gwamnan a matsayin mutumin kirki kuma ya yaba masa kan shirin hada kan kowa wuri guda don amfanin jam’iyya da jihar baki daya.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

Yace:

“Mun zo nan ne don yin magana kan rashin jin dadin mu. Abin da muke so da abin da ba mu so.
“Mata da maza, idan ba mu hade ba ba za mu cimma komai ba tare. Idan bai kai kanka ba yau, ba yana nufin ba zai kai kanka ba gobe.”

Ya shawarci gwamnan da ya yi taka tsantsan da mutanen da za su so yin amfani da madaukakin ofishinsa don biyan bukatun kansu, wanda a ƙarshe zai iya jefa jam’iyya gaba ɗaya cikin rikici mara amfani.

Tsohon shugaban jam'iyyar, wanda bai yarda da ra'ayin cewa dole ne mutum ya kasance yana da tsari kafin ya nemi mukamin siyasa ba, ya ba da misalin wasu fitattun 'yan siyasa da suka kai ga ci gaban rayuwarsu ba tare da fara samun tsarin siyasa a kasa ba.

Ya ce karfafawa kan tsare-tsare na iya rusa tushen siyasa mai inganci, kuma mutanen da suka gabata sun lalata tunanin samun tsari kafin shiga siyasa, zai fi kyau ga ci gaban siyasar jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta sallami shugabanta da ya ce Buhari ya mutu kowa ya huta

Rikicin cikin gida zai iya tarwatsa mu, Kwankwaso ya ja kunnen shugabannin PDP

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP ya na iya tarwatsa jam'iyyar baki daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Kwankwaso ya ce ba a bukatar irin wannan rikicin a wannan lokacin da jam'iyyar ke fama da rasa mambobin ta.

A yayin zantawa da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce tuni ya nisanta kan sa daga dukkan wani rikici kuma kamar yadda ya ce, wadanda ba kwararrun 'yan siyasa ba ne suka hura wutar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng