2023: Kada ku bari Atiku ya yi maku asarar tikitinku, kungiya ta gargadi PDP

2023: Kada ku bari Atiku ya yi maku asarar tikitinku, kungiya ta gargadi PDP

  • Wata kungiyar magoya bayan PDP ta gargadi jam'iyyar a kan baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar tikitin takarar shugaban kasa
  • A cewar kungiyar mai suna PDP Action 2023, mika wa Atiku tikitin kamar asara ne domin jam'iyyar ba za ta kai labari ba idon ta tsayar da shi
  • Ta kuma zargi dan takarar na zaben 2019 da guduwa Dubai bayan zabe sannan ya dawo a yanzu da aka kusa zaben fidda gwani

Abuja - Magoya bayan jam'iyyar Peoples Democratic Party, a karkashin inuwar PDP Action 2023, sun yi kira ga jam'iyyar da ta guji maimaita kuskuren asarar tikitin takarar Shugaban kasa kan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Kungiyar ta yi wannan roko ne a cikin wata sanarwa mai taken, “Kada Atiku Ya sake Bata tikitin PDP” wanda Shugabanta na kasa, Dakta Rufus Omeire, ya sanya wa hannu a Abuja, a ranar Laraba, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa: Kungiyar IPOB ta tanadi makamai da bama-bamai a fadin Najeriya

2023: Kada ku bari Atiku ya yi maku asarar tikitinku, kungiya ta gargadi PDP
Kungiya ta gargadi PDP a kan ba Atiku tikitin takarar shugaban kasa a 2023 Hoto: The Cable
Asali: UGC

Kungiyar ta kara gargadin tsohon mataimakin shugaban kasar da kada ya yaudari mambobin jam'iyyar a karo na biyu, jaridar Thisday ta ruwaito.

Omeire ya ce:

“Kungiyar PDP Action 2023 ta sake yin gargadin cewa, ba wa Atiku Abubakar wani dama a matsayin dan takarar Shugaban kasa na PDP shi zai tabbatar da kayen da PDP za ta sha a 2023, kuma tana gargadin tsohon Mataimakin Shugaban kasar da kar ya yaudari‘ ya’yan PDP a karo na biyu.
"A cikin Sanarwarmu ta ƙarshe, mun nuna rashin jin daɗi ga Atiku saboda ya yi watsi da membobin PDP ta hanyar guduwa don komawa da zama a Dubai bayan zaɓe, yana kare kansa daga membobin PDP, kawai sai ga shi ya sake bayyana yanzu lokacin da zaɓen fidda gwani na Shugaban ƙasa ya kusa.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Jerin manyan 'yan PDP 3 da za su yi gasar neman tikitin Jam'iyyar

“A martanin da ya mayar, mun yi mamaki da ganin Atiku ya yi ikirarin cewa ya dade baya Najeriya ne saboda yana kokarin samun digiri daga Jami'ar Cambridge.
"Sabanin haka, duk kasar tana sane da cewa ya koma Dubai, inda har ma ya yi tallar rigakafin korona sosai tun kafin talakawan Najeriya su samu rigakafin cutar.”

Kungiyar ta ci gaba da cewa:

“Rashin kunya ne Atiku ya yi ikirarin cewa yana makaranta a Cambridge, London lokacin da a zahiri yake zaune a Dubai.
"Idan ya yi rajista a Jami'ar Cambridge, zai iya yin karatunsa sosai daga Najeriya."

Kokarin samun martani daga ofishin yada labaran tsohon mataimakin shugaban kasar ya ci tura. Kiran da aka yiwa layin hadiminsa, Mazi Paul Ibe ya nuna a kashe wayar take.

Shugabancin 2023: Jerin manyan 'yan PDP 3 da za su yi gasar neman tikitin Jam'iyyar

A wani labarin, mun ji cewa yayin da zaben shugaban kasa na 2023 ke karatowa, 'yan siyasa a fadin jam’iyyun siyasa sun fara hararar tikitin jam’iyyarsu domin zama yan takara.

Kara karanta wannan

2023: A karshe Tinubu ya samu daidai da shi yayin da jiga-jigan PDP suka marawa tsohon gwamna baya

Ga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), akwai ikirarin cewa manyan sunaye za su sake fitowa kamar yadda aka yi a zaben 2019.

Wasu daga cikin manyan jiga-jigan da ake sa ran za su fafata don neman tikitin takarar shugaban kasa na PDP su ne Bukola Saraki, Atiku Abubakar, da Aminu Tambuwal, duk da cewa har yanzu ba su nuna sha’awarsu a takarar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng