Gwamna ya tono dalilan da suke jawo kalubalen tsaro a siyasance a Najeriya

Gwamna ya tono dalilan da suke jawo kalubalen tsaro a siyasance a Najeriya

  • Gwamnan jihar Bayelsa ya bayyana dalilin da yasa Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro
  • Ya ce, wasu 'yan siyasa marasa kima su ke amfani da damar da suke dashi wajen lalata kasa
  • A cewarsa, kasar ba wai matsalar tsaro da aka sani kadai fuskanta ba, tana kuma fuskantar matsalar tsaro na siyasa

Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Mista Douye Diri, a ranar Talata 31 ga watan Agusta ya ce Najeriya ta shiga halin kalubalen tsaro a siyasance ne saboda yawancin 'yan siyasa suna siyasar son kai don cutar da amfanin al'umma baki daya.

Diri ya kuma ce kasar ta rarrabu fiye da kowane lokaci saboda son kai, kabilanci da rashin kishin kasa da na albarkatun dan adam da na kasa, Punch ta ruwaito.

Gwamna ya tono dalilan da suke jawo kalubalen tsaro a siyasance a Najeriya
Gwamnan jihar Bayelsa | Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a Babban Taron Gudanarwa na Yankin Kudu maso Kudu wanda Cibiyar Gudanarwa ta Najeriya ta shirya a Yenagoa tare da taken, 'Sarrafa kalubalen tsaro don hadin kan kasa a Najeriya: Matsalar Kudu maso Kudu.'

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Neja: Dole ne a ilmantar da 'yan Najeriya idan ana son bindiganci ya kare

Diri ya ce baya ga tashin hankali, garkuwa da mutane da sauran kalubalen tsaro, kasar na fama da abin da ya bayyana a matsayin rashin tsaro na siyasa, zamantakewa, kiwon lafiya da abinci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan, wanda ya yi magana ta bakin mataimakinsa, Mista Lawrence Ewhrudjakpo ya nuna cewa matakin rashin tsaro da ke addabar kasar a halin yanzu ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

A cewarsa:

"Rashin tsaro yana zuwa ta hanyoyi daban-daban. Ba wai kawai rashin tsaro bane; hukumomin tsaron mu suna fama da bindiganci, tayar da kayar baya, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka; muna da rashin tsaro da ke fuskantar tsarin siyasarmu.
"A cikin wannan kasa, muna da yanayin da yawancin 'yan siyasa ba su da wata kima amma kawai suna biyan bukatun kansu ne.
"Muddin aka kare bukatarsu ko aka biya ta, za su iya barnata duk wani sakamako har ma da muradin mutanen da suke jagoranta. Don haka ne wasu daga cikinsu za su iya canzawa kamar hawainiya da tsallake jirgi cikin sauki.”

Kara karanta wannan

Garabasa: Matashi na neman budurwar da zata so shi, zai ba ta albashin N150k duk wata

Ita ma da take jawabi, Shugabar Cibiyar Gudanarwa ta Najeriya, Misis Patience Anabor, ta lura cewa matakin rashin tsaro na yanzu ya haifar da babbar illa ga tattalin arzikin kasa.

Tsohon gwamnan Neja: Dole ne a ilmantar da 'yan Najeriya idan ana son bindiganci ya kare

Tsohon gwamnan jihar Neja, Mu'azu Babangida Aliyu, ya ce ba za a iya kawo karshen ta'addanci da tayar da kayar baya ba a Njierya idan har dimbin 'yan Najeriya ba su zama masu ilimi ba.

Aliyu ya bayyana haka ne yayin wani taro a Gidauniyar Sir Ahmadu Bello na Zauren Jagorancin shekarar 2021 da aka gudanar a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, karancin ilimin yadda za a ba da bayanai ga hukumomin ta hanyar al'ummomi kan masu aikata laifuka da ke ratsawa cikin yankunansu shi ya jawo rashin tattara bayanan sirri.

A kalamansa, cewa ya yi:

Kara karanta wannan

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

"Idan ba mu ilmantar da jama'armu ba, Boko Haram da sauran aikin ta'addanci ba zasu kare ba saboda za a samu mutane masu son yin fafutukar neman hakkinsu kuma suna ganin hakan daidai ne ta hanyar fada saboda kuna sanye da tufafi mafi kyau."

'Yan APC sun roki Buhari ya mika kujerarsa zuwa kudancin Najeriya a zaben 2023

A wani labarin, Wata kungiya a jam'iyyar APC mai suna South East Mandate (SEM), ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saukaka hanyoyin zabar dan takarar shugaban kasa daga amintattun mambobin jam’iyyar na Kudu maso Gabas a zaben 2023.

Ta ce manufarta ita ce tabbatar da an samu shugaba daga yankin na Kudu maso Gabas a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari.

Kungiyar ta bukaci jam’iyyun siyasa a Najeriya da su mika tikitin takarar shugaban kasar nan zuwa Kudu maso Gabas bisa adalci, gaskiya da lamiri mai kyau.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.