Abin da gwamnatin Tinubu Ta Ce kan ba Hukumar Bogi Kudi, Bude Asusu a CBN
- Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya wanke gwamnatin Bola Ahmed Tinubu daga zargin cewa ta rika daukar nauyin hukumar PFIPC da aka ce ta bogi ce
- Hukumar ta bayyana cewa PFIPC ba ta da asusun aiki a Babban Bankin Najeriya (CBN), don haka ba za a iya tura mata kudi ba kamar yadda ake ikirari
- Ofishin bayani kan zargin cewa ana biyan ma'aikatan PFIPC albashi, tana mai cewa ba a kammala ka'idojin daukar ma'aikata ba tukunna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF) ya bayyana cewa babu wani kudin gwamnati da aka taba fitar wa da sunan hukumar PFIPC, wacce ake ta ce-ce-ku-ce a kanta.
Ofishin ya kuma bayyana cewa PFIPC ba ta da asusun aiki a Babban Bankin Najeriya (CBN), sabanin rahotannin da suka yi ikirarin cewa an tura mata kudi tare da biyan ma'aikatanta albashi.

Source: Facebook
Arise News ta wallafa cewa daraktan yada labarai da hulda da jama'a na OAGF, Bawa Mokwa, ya ce majalisar ba ta taba samun kasafin kudi ko wata rabon kudade daga gwamnatin tarayya ba.
Yadda PFIPC ya fara neman asusun CBN
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Bawa Mokwa ya bayyana cewa an taba fara kokarin bude mata asusu a CBN, amma ba a kammala aikin ba saboda ba a gabatar da duk takardun da ake bukata ba.
A cewarsa, ba za a iya bude asusu a CBN ba tare da amincewar Akanta Janar na Tarayya ba, tare da jaddada cewa babu wannan magana a kasa.

Source: Facebook
Mokwa ya ce wanda ya kafa hukumar, Adeniyi Adeyemi, ya gabatar wa OAGF da takardar nadin aiki, amma takardar tana da alaka da wata hukuma da aka kafa a baya ba PFIPC ba.
Ya ce an fara aikin bude asusun ne bisa takardar da aka gabatar, amma aka dakatar da shi saboda ba a gabatar da sunayen jami'an da za su kasance masu sanya hannu kan asusun ba.
Mokwa ya ce:
"Har zuwa yau, asusun bai fara aiki ba. Bai taba karbar ko sisi ba saboda ba a kammala bude shi ba."
Ba PFIPC a kasafin kudi - Gwamnati
Ya kuma bayyana cewa ba a saka PFIPC cikin kasafin kudin gwamnatin tarayya ba, yana mai cewa ana sa ran batun samar mata da kudade ne kawai a kasafin shekarar 2026, wanda har yanzu ba a fara aiwatar da shi ba.
Mokwa bayyana cewa kafin kowace hukuma ta gwamnatin tarayya ta dauki ma'aikata tare da saka sunayensu a tsarin biyan albashin gwamnati (IPPIS), dole ne ta samu amincewa daga hukumomi da dama.
Ya ce ba za a iya saka sunan ko mutum daya a tsarin biyan albashi ba tare da wadannan amincewa ba, yana mai jaddada cewa PFIPC ba ta kammala ko daya daga cikin wadannan matakai ba.
Ya sanda sun kama uban 'shugaban' PFIPC
A baya, mun wallafa cewa rahotanni sun bayyana cewa rundunar yan sandan Najeriya ta kama mahaifin Prince Adeyemi Adeniyi kan binciken da ake yi kan zargin kirkirar hukuma PFIPC.
Lamarin a fara jawo martani inda lauyan kare hakkin bil'adama, Femi Falana (SAN), ya ce babu wata doka a Najeriya da ta bayar da dama a kan a kama dan uwa a madadin wanda ake nema.
Wannan an zuwa ne a lokacin da Adeyemi ya amsa cewa zai halarci kotu, sannan za a wanke shi kan zargin cewa ya yi gaban kansa wajen kafa hukumar ba tare da sahalewar gwamnati ba.
Asali: Legit.ng


