Duk da Ana Kashe Ƴan Najeriya a Afrika Ta Kudu, Majalisa Ta ki Yarda a Kwace MTN, DSTV

Duk da Ana Kashe Ƴan Najeriya a Afrika Ta Kudu, Majalisa Ta ki Yarda a Kwace MTN, DSTV

  • Majalisar Dattawa ta yi watsi da bukatar kwace MTN da DStv duk da ana ci gaba da kai hare-haren kyamar baki kan 'yan Najeriya a Afirka ta Kudu
  • Sanatoci sun bukaci gwamnatin tarayya ta kara matsin lamba ta fuskar diflomasiyya domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya a can
  • Majalisar ta nemi gwamnatin Afirka ta Kudu ta gurfanar da masu kai hare-hare tare da ba Najeriya tabbacin kare 'yan kasarta nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi na kwace kamfanonin MTN da DStv mallakin 'yan Afirka ta Kudu a matsayin martani ga hare-haren xenophobia da ake ci gaba da kai wa 'yan Najeriya a kasar.

Sai dai majalisar ta yi Allah wadai da hare-haren, tare da bukatar gwamnatin tarayya ta kara kaimi wajen amfani da hanyoyin diflomasiyya domin kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu.

Kara karanta wannan

Majalisa na neman taka wa Tinubu birki kan tubabbun yan ta'adda a Najeriya

Majalisar Dattawa ta yi watsi da kiran kwace kamfanonin MTN, DSTV.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya shigo zauren majalisa don fara zama. Hoto: The Nigeria Senate
Source: Twitter

Martanin majalisa kan hare-haren kyamar baki

Wannan ne karo na biyu cikin watanni biyu da Majalisar Dattawa ke tattauna batun hare-haren kyamar baki kan 'yan Najeriya da sauran 'yan kasashen Afirka da ke zaune a Afirka ta Kudu, in ji rahoton Vanguard.

Matsayar majalisar ta biyo bayan kudirin da Sanata Asuquo Ekpenyong mai wakiltar Cross River ta Kudu ya gabatar mai taken bukatar dakile hare-haren kyamar baki da cin zarafin 'yan Najeriya da sauran 'yan Afirka a Afirka ta Kudu.

Kudirin ya biyo bayan sabon salon hare-haren da aka fara kai wa bakin haure bayan wa'adin ranar 30 ga Yunin 2026 da wasu kungiyoyin sa-kai suka bayar na su bar kasar.

Shawarwarin majalisa ga gwamnatin Tinubu

Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta hannun Ma'aikatar Harkokin Waje da Babban Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Afirka ta Kudu ta nemi gwamnatin kasar ta bayar da rubutacciyar tabbaci kan tsaron 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Rahoton WFP: ADC ta zargi Tinubu da jefa miliyoyin mutane cikin yunwa a jihohin Arewa 9

Haka kuma ta bukaci gwamnatin Afirka ta Kudu ta kama tare da gurfanar da duk wadanda ake zargi da kashe-kashe, cin zarafi, kwace dukiyoyi da kuma aiwatar da dokokin shige da fice ba bisa ka'ida ba.

Majalisar ta kuma bukaci Ma'aikatar Harkokin Waje, Hukumar 'Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NiDCOM) da Ofishin Jakadancin Najeriya su samar da cikakken rajistar 'yan Najeriya da suka mutu, suka jikkata, suka rasa matsuguni ko dukiyoyi saboda hare-haren.

An nemi Najeriya ta tuntuni kungiyar AU

A cewar sanatocin, hakan zai taimaka wajen neman diyya da tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Har ila yau, majalisar ta bukaci gwamnatin Najeriya ta hada kai da sauran kasashen Afirka da abin ya shafa tare da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) domin samar da tsarin gargadi da sa ido kan hare-haren xenophobia a nahiyar.

Daga karshe, ta umurci kwamitocin harkokin waje da na 'yan Najeriya mazauna kasashen waje su duba yadda aka aiwatar da kudurorin da majalisar ta yanke tun ranar 5 ga Mayun 2026, sannan su gabatar da rahoto cikin makonni hudu kan matakan da aka dauka da kuma abin da ya rage a yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com