Zaben 2023: Gwamnonin APC 5 da ka iya tsayawa takara a gefen Goodluck Jonathan
Rahotanni sun bayyana cewa Goodluck Ebele Jonathan na da sha’awar shiga jerin 'yan takarar shugaban kasa na 2023 da ake ta magana akai. Idan aka samu dalili tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana tsayawa takara, daya daga cikin wasu gwamnonin Najeriya da ke na iya zama abokin tafiyar takarar.
Akalla biyar daga cikin wadannan gwamnonin, dukkansu daga yankin Arewa, jiga-jigan jam'iyyar APC ne, wadanda alamu na nuna suna da alaka ta kusa da wasu 'yan siyasar da ke hangen kujerar shugaban kasa a 2023.
1. Gwamna Nasir El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna, ko shakka babu, yana morar kawancensa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma yana da manyan madafun iko a yankin da kuma cikin jam’iyya mai mulki.
Fiye da sau daya, an samu hotunan Gwamna El-Rufai da wasu manyan APC kamar takwaransa na Ebonyi, Dave Umahi, Adams Oshiomhole, da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo na takarar 2023 sun cika titunan Kaduna.
Sai dai, a bangare gida, gwamnan ya nisanta kansa daga irin wannan wadanann hotuna.
2. Gwamna Yahaya Bello
Wasu masu sharhi kan al'amuran siyasa sun bayyana shi a matsayin daya daga cikin masu kare shugaban kasa, gwamnan na Kogi ya yi alfahari da cewa, duba da kwazonsa, matasa a Najeriya sun bukaci ya tsaya takarar shugaban kasa.
Kamar yadda Premium Times ta ruwaito a farkon watan Agusta, gwamnan, duk da cewa shi Musulmi ne mai kishin addini, ya samu babban goyon baya daga wata kungiyar Kiristoci, Christian Youth Leadership Network, a wani buri wanda har yanzu bai bayyana ba.
3. Gwamna Babagana Zulum
Kokarin da Zulum ya yi na shawo kan barnar masu tayar da kayar baya a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin kasar ya ba shi damar zama jagora nagari wanda ba ya bukatar yakin neman zabe mai yawa idan ya yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasa.
A zahiri, a lokacin da ta'addanci ya ta'zzara a jihar, Guardian ta ba da rahoton cewa gwamnan kuma farfesa ya shiga wani irin yanayi na rashin fahimtar juna da sojoji inda ya zargi Sojojin Najeriya da rashin kishin kasa wajen dakile Boko Haram.
4. Gwamna Abdullahi Ganduje
Ba tare da duba game da zargin cin hanci da rashawa yayin da ake shirin zaben gwamna a jihar Kano na 2019 ba, ana daukar Gwamna Ganduje a matsayin daya daga cikin manyan abokan tafiyaa fadar shugaban kasa.
Saboda haka, ba zai sha wata wahala ba wajen isa ga fadar shugaban kasa da shirin tsayawa wata babbar takara ba.
5. Gwamna Bello Masari
Menene kuma wa zai iya hana dan uwan Shugaba Buhari wanda ke rike da madafun iko a jihar Katsina wani mukami idan ya yarda ya hada kai da sauran masu fafatawa a yakin neman zabe?
Kwanaki bayan ganawa da Tinubu, shahararren gwamnan APC ya magantu akan kudirin takarar shugaban kasa
Gwamna Masari a halin yanzu shine shugaban yankin Arewa maso yamma kuma yana cikin manyan 'yan siyasa daga shiyyar wadanda ke cikin jerin nagartattu a littafin shugaban kasa.
Babbar magana: 'Yan APC sama da 50,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Adamawa
A wani labarin, sama da mambobin jam’iyyar APC 50,000 ciki har da tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, Mista Kobis Ari Themnu, sun koma PDP a ranar Asabar, 4 ga watan Satumba.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ya tarbe su a dandalin Ribadu Square na taro a Yola ya zarge su da yin imani da kuma daidaita amincin su ga jam'iyyar da ta gaza tun farko, inji rahoton jdairdar Leadership.
Sai dai Atiku ya ce kuskuren su na kasancewa a cikin APC yanzu an gafarta musu, sannan ya kara tabbatar da cewa PDP ta shirya ta karbi mulkin kasar nan a zaben 2023. Read more: https://hausa.legit.ng/1432813-babbar-magana-yan-apc-sama-da-50000-sun-sauya-sheka-zuwa-pdp-a-adamawa.html
Asali: Legit.ng