Mai Martaba Sarkin Ilorin Ya Yi wa 'Yan Takarar APC Addu'a Ta Musamman gabanin Zaben 2027

Mai Martaba Sarkin Ilorin Ya Yi wa 'Yan Takarar APC Addu'a Ta Musamman gabanin Zaben 2027

  • Sarkin Ilorin da ke jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya yi wa dukkan 'yan takarar APC addu'ar samun nasara a zaɓen 2027
  • Ya ce Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi ayyukan ci gaba da suka bayyana ga kowa, don haka ya kamata a saka masa
  • Rahotanni sun nuna dubban magoya bayan APC da yan takara sun kai ziyara fadar Sarkin domin neman albarka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara, Nigeria - Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya yi wa 'yan takarar jam'iyyar APC na jihar Kwara addu'ar samun nasara a babban zaɓen 2027.

Sarkin ya bayyana goyon bayansa bisa abin da ya kira kyakkyawan jagoranci da nasarorin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, wanda shi ne jagoran APC a jihar Kwara.

Sarkin Ilorin.
Mai martaba Sarkin Ilorin da ke jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari Hoto: Ilorin Emirate
Source: Twitter

Punch ta ce Sarkin ya bayyana hakan ne a yau Litinin lokacin da dubban shugabanni da magoya bayan APC suka kai masa ziyara domin gabatar masa da 'yan takarar jam'iyyar tare da neman addu'a da albarka.

Kara karanta wannan

Gwamnan Alia ya bugi kirji, ya fadawa Tinubu yawan kuri'un da zai samu a Benue

Magoya bayan APC sun cika fadar sarki

Shugaban APC na jihar Kwara, Sunday Fagbemi, ne ya jagoranci tawagar, wadda ta haɗa da manyan jiga-jigan jam'iyyar da kuma dukkan 'yan takararta.

Cikin tawagar akwai Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara kuma ɗan takarar gwamna na APC, Rt. Hon. Yakubu Danladi, da 'yan takarar Sanata, na Majalisar Wakilai da kuma na Majalisar Dokokin Jiha.

Da yake jawabi, Sarkin Ilorin ya ce ya yi matuƙar farin ciki da yadda magoya bayan APC suka cika harabar fadarsa.

Ya kuma bayyana Gwamna AbdulRazaq a matsayin shugaba mai kyawawan halaye da manyan nasarori, kamar yadda Leadership ta kawo.

Sarkin ya yabawa Gwamna AbdulRazaq

Ya yabawa gwamnan kan shirye-shiryen ci gaban da yake aiwatarwa tare da yi masa addu'ar ci gaba da samun nasara, haka kuma ya yi wa dukkan 'yan takarar APC addu'ar samun nasara a zaɓe.

Ya ce:

"Tun da safe harabar fadana ta cika da magoya bayanku. Shin yau ranar zaɓe ce ko kuwa ziyara kuka zo yi? Ina roƙon Allah ya albarkaci duk wani mataki da Sadauna Ngeri (Gwamna) ya ɗauka."

Kara karanta wannan

2027: Maza da mata sun fito gangamin nuna goyon baya ga tazarcen Tinubu a Kwara

"Duk wanda ya ga alheri ya ƙi faɗarsa ba mai gaskiya ba ne. Ƙarya ba ta da wurin ɓuya, abin da muke gani a ƙasa gaskiya ne. Duk wanda ya yi alheri, mu faɗi haka. Gwamnan ya yi aiki sosai."
"Daga Gwamna AbdulRazaq zuwa sauran 'yan takarar jam'iyyar, Allah Ya ba ku nasara a zaɓe. Allah Ya sa kada a kunyata ku."
Gwamna AbdulRahman.
Gwamnan jihar Kwara, AbsulRahman AbdulRazaq yana jawabi a wurin taro Hoto: @AARahman
Source: Facebook

APC ta fara gangamin magoya baya

A Wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC a jihar Kwara ta fara gangamin neman goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu da kuma shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Gangamin, wanda ƙungiyar Kwara Progressives ta shirya ƙarƙashin taken "Kwara Ndupe (Kwara na godiya)", ya haɗa shugabannin jam'iyyar, 'yan takara da dubban magoya baya da suka yi jerin gwano a manyan titunan Ilorin .

Masu shirya taron sun bayyana cewa manufar gangamin ita ce murnar nasarar zaɓen fidda gwani da kuma fara shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen 2027

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262