Kashe-kashen Benue: An nemi DSS ta binciki Ministan Buhari

Kashe-kashen Benue: An nemi DSS ta binciki Ministan Buhari

  • PDP ta yi kira ga hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS da ta duba rawar ganin da ake zargin Sanata George Akume ya taka a kisan Benue
  • Wannan kiran ya zo ne kwana guda bayan Akume, Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnatoci, ya roki EFCC da ta binciki Gwamna Samuel Ortom
  • Jam'iyyar ta kuma bukaci hukumar da ta binciki Akume kan cin hanci da rashawa a Benue yayin da yake gwamna

Benue - Ga dukkan alamu abun ya juyo kan ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci, Sanata George Akume, kan kiran da ya yi wa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na su binciki gwamna Samuel Ortom.

Dangane da abin da Akume ya gabatar, Jam’iyyar PDP ta nemi hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta bincike shi kan zargin hannu a kisan Benue, jaridar This Day ta rahoto.

Kara karanta wannan

NDA: Babban malamin adddini ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya, ya ce karin matsaloli na tafe

Kashe-kashen Benue: An nemi DSS ta binciki Ministan Buhari
PDP nemi DSS ta binciki Ministan Buhari, ore Akume Hoto: Benue State Government
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa ta hannun sakataren yada labaran ta na kasa, Kola Ologbondiyan, PDP ta ce rokon da ta yi wa DSS ya dogara ne kan tunanin Akume game da kashe-kashen da ke faruwa a jihar, jaridar Punch ta ruwaito.

Yayin da yake kira ga tsohon gwamnan da ya fito ya wanke kansa kan zargin da ake yi masa a kashe-kashen, PDP ta kuma bukaci hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da ta bincike shi kan karkatar da kudaden gwamnati a lokacin gwamnatinsa.

Sanarwar ta ce:

“Sanata Akume ya tofa albarkacin bakinsa kan wadanda aka kashe tare da yin tozarci kan tunanin mutanen Benue kuma tarihi zai dunga tunawa da shi koyaushe akan wannan mataki.

Kara karanta wannan

Akume ya roki EFCC ta yi ram da gwamnan Benue Ortom ta bincikeshi kan wasu kudi

"Jam'iyyarmu, da ke tare da jama'ar jihar Benue, tana neman a sanya Sanata Akume ya fito ya wanke kansa saboda ayyukansa sun kara tabbatar da haka ta hanyar mugun harin da ya kai wa Gwamna Ortom."

Akume ya roki EFCC ta yi ram da gwamnan Benue Ortom ta bincikeshi kan wasu kudi.

A baya mun kawo cewa ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci, Sanata George Akume, ya nemi hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su binciki Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue.

Akume, tsohon gwamnan jihar Benue, ya yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin 30 ga watan Agusta.

Ya kuma nemi Ortom da ya daina fadan bakaken maganganu kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel