Allah zai bamu shugaba kamar Buhari a 2023, inji gwamnan Ebonyi

Allah zai bamu shugaba kamar Buhari a 2023, inji gwamnan Ebonyi

  • Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya nuna yakinin cewa Allah zai ba kasar Najeriya shugaba mai kyakkyawar zuciya kamar na Buhari a 2023
  • Umahi ya kuma bayyana cewa mambobin jam’iyyun siyasa daban-daban daga Kudu maso Gabas suna aiki don ganin an mika tikitin takarar zuwa yankinsu
  • Sai dai ya ce yayi wuri da yawa da za a fara tattauna zabe na gaba tun daga yanzu

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana fatan wanda ke da “kyakkyawar zuciya” kamar Shugaba Muhammadu Buhari zai fito a matsayin wanda zai maye gurbinsa a 2023, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Ya fadi hakan ne duk da cewar ya ce ya yi wuri sosai da za a shiga harkokin siyasar 2023 kamar yadda ya lura cewa hakan zai zama shagala a bangaren shugaban kasa da gwamnonin jihohi.

Allah zai bamu shugaba kamar Buhari a 2023, inji gwamnan Ebonyi
Gwamna Dave Umahi ya nuna fatan cewa Allah zai sake bamu shugaban kasa kamar Buhari a 2023
Asali: UGC

Gwamnan, wanda ya amsa tambayoyi daga manema labarai bayan ziyarar da ya kai wa Shugaba Buhari a fadar shugaban kasa, Abuja a ranar Litinin, ya kuma lura cewa membobin jam’iyyun siyasa daban-daban daga Kudu maso Gabas suna aiki a cikin jam’iyyunsu don tabbatar da ganin cewa an mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa yankin.

Jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito cewa da aka tambaye shi ko shugabannin Kudu-maso-Gabas suna aiki don ganin manyan jam’iyyun siyasa sun mika tikitin shugabanci zuwa yankin, sai ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“To, a gare ni, nafi mayar da hankali sosai wajen kammala ayyukana. Kuma zan duba harkar siyasa idan wa'adin mulkina ya rage shekara guda, wanda zai kasance daga 29 ga Mayun 2022. Kuma ina tsammanin haka yake ga sauran gwamnonin Kudu maso Gabas da na APC.

“Matsayi na game da abin da kuke tambaya shi ne mutanen mu da ke cikin wadancan jam’iyyun siyasa suna yin kokari wajen siyar da bukatar Kudu maso Gabas don samar da shugaban kasa na gaba.
"Amma ina tsammanin bai kamata duka gwamnonin da shugaban kasa su shagala ba. Idan aka yi zabe kuma aka ci nasara, ya kamata ya zama mulki. Amma a kasar nan, da zarar an kammala zabe, abu na gaba da za a fara shi ne cewa ana yaudarar talakawa.
“Don haka, wadanda aikinsu siyasa ne kuma wadanda ba sa cikin zababbun mukamai, ko mukaman da aka nada suna da kowane lokaci da damar yin wannan kiran. Kuma ina tsammanin suna yin hakan kuma suna yin shi sosai.
“Amma ina ci gaba da fadin cewa mulki na Allah ne. Kuma Allah zai ba mu shugaba na gaba mai kyakkyawar zuciya kamar Shugaba Buhari don amfanin ƙasar nan.

"Muna bukatar zabin Allah bisa ga namu zabin shugabar shugaban, don maslaha da haɗin kan ƙasar nan."

Zaka Zubar da Mutuncinka a Idon Yan Najeriya Matukar Ka Sauya Sheka Zuwa APC, Jigon PDP Ya Faɗawa Jonathan

A wani labarin, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dr Okwesilieze Nwodo, ya gargaɗi tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan kada yayi gangancin komawa jam'iyya mai mulki APC, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Nwodo ya bayyana cewa matukar Jonathan ya koma APC to ya zubar da ragowar mutuncinsa da kimarsa a idon yan Najeriya.

Yace tsohon shugaban ba zai iya kawo sauyi a jam'iyyar ba domin komawarsa zata ƙara shagwaba yan APC ne su cigaba da ɗaukar abinda duke yi dai dai ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel