Zaben Kananan Hukumomi: Yan Daba Sun Sace Na'urar Zaɓe Sama da 40 a Kaduna, El-Rufa'i Ya Magantu

Zaben Kananan Hukumomi: Yan Daba Sun Sace Na'urar Zaɓe Sama da 40 a Kaduna, El-Rufa'i Ya Magantu

  • Hukumar zaben jihar Kaduna (KADSIECOM) tace an lalata tare da sace wasu na'urorin da aka tanaza don zaben kananan hukumomi
  • Shugabar Hukumar, Saratu Dikko, tace an kaiwa ma'aikata hari a kananan hukumomin Giwa da Igabi
  • Gwamna El-Rufa'i ya koka kan rashin kawo kayayyakin zaɓe zuwa runfunan zaɓe da wuri

Kaduna - Wasu da ake zargin yan daban siyasa ne sun farfasa na'urar kaɗa kuri'a (EVM) guda 11 yayin zaɓen kananan hukumonin Kaduna a Igabi da Giwa, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Shugabar hukumar zaɓe ta jihar Kaduna (KADSIECOM), Saratu Audu-Dikko, tace an sace na'urar EVM 41 a yayin zaben wanda ya gudana ranar Asabar.

Na'urar EVM
Zaben Kananan Hukumomi: Yan Daba Sun Sace Na'urar Zaɓe Sama da 40 a Kaduna, El-Rufa'i Ya Magantu Hoto: thenewsnigeria.com.ng
Asali: UGC

A jawabinta tace:

"An sace na'ura 30 a a Kwarau, karamar hukumar Igabi, yayin da aka lalata wasu guda 9 a Panhauya, dake karamar hukumar Giwa."

Kara karanta wannan

Zaben kananan hukumomin Kaduna: PDP ta lallasa APC a akwatin mazabar Gwamna El-Rufa'i

"Hakazalika, maharan sun lalata wasu kayayyakin zaɓen, sannan suka lakaɗawa direba da wasu ma'aikatan mu duka, waɗanda suke tare da kayan."

Shugabar KADSIECOM tace an kaiwa ma'aikatan hukumar hari, daga ciki harda ma'aikatan wucin gadi da ta ɗauki domin gudanar da zaɓen.

Wane mataki gwamnatin Kaduna ta ɗauka?

Kafin haka, gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya bayyana damuwarsa kan yanayin rashin hitowar jama'a runfunan zaɓe don kaɗa kuri'a.

Da yake jawabi bayan ya danna kuri'arsa, El-Rufa'i ya ɗora alhakin rashin hitowar jama'a da rashin isowar kayayyakin zaɓe da wuri.

Sai dai duk da haka, gwamnan yace an samu cigaba a zaɓen idan aka kwatanta da wanda aka gudanar a shekarar 2018.

APC ta al'umma ce, ba zata shirya maguɗi ba

A cewar El-Rufa'i, na'urar EVM da aka samar domin zaɓen ba zata yarda kowane mutum ya kaɗa kuri'a sama da ɗaya ba.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An Ɗage Zaɓukan Ƙananan Hukumomi 4 a Jihar Kaduna

Yace ba dole bane sai APC ta lashe kowace kujera don jam'iyyar ta na aiki ne domin al'umma, sabili da haka su zaɓi wanda suke so ya jagorance su.

"Da katin ka zaka bude wurin jefa kuri'a a na'urar EVM, bayan an tantance ka, daga nan kuma sauran aikin bai wuce sakan 15 ba, abin yana da sauri kuma zaka ga takardar abunda ka zaɓa ta fito."

A wani labarin kuma Tsohon Sakataren Gwamnati Tare da Wasu Mutum 50,000 Sun Fice Daga APC, Sun Koma PDP

Sama da mutum 50,000 mambobin jam'iyyar APC, tare da tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, Mr Kobis Ari Themnu, sun sauya sheka zuwa PDP, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, shine ya tarbe su a babban filin taro na Ribaɗu Square, jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel