Shugabancin 2023: An bayyana jigon PDP da ya shirya sosai don kwace mulki daga APC

Shugabancin 2023: An bayyana jigon PDP da ya shirya sosai don kwace mulki daga APC

  • Wata kungiyar siyasa, Amalgamated Atiku Support Group (AASG), ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku a matsayin wanda tafi so ya zama shugaban kasa a 2023
  • Jagoran kungiyar na kasa, Oladimeji Fabiyi, ya ce dan siyasar haifaffen Adamawa ne mafi shiri da zai iya korar APC daga Aso Villa a zabe mai zuwa
  • Fabiyi ya yi watsi da hasashen cewa bai kamata a tsayar da Atiku a matsayin dan takarar PDP ba saboda yawan shekarunsa

Wata kungiya a karkashin inuwar Amalgamated Atiku Support Group ta nuna goyon bayanta ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar don ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Jagoran kungiyar na kasa, Oladimeji Fabiyi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 3 ga watan Satumba, ya ce Atiku shi ne dan siyasa mafi shiri kuma gogaggen dan siyasa da zai kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore

Shugabancin 2023: An bayyana jigon PDP da ya shirya sosai don kwace mulki daga APC
Wata kungiya ta ayyana Atiku a matsayin wanda ya cancanci karbar mulki a 2023 Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Fabiyi ya kuma yi Allah wadai da sanarwar baya-bayan nan da aka danganta ga wata kungiya da ke ba da shawarar cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kada ta tsayar da Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a babban zabe mai zuwa.

Ya ce kungiyar da ba a bayyana sunanta ba ta kaddamar da adawa kan Atiku amma ya jaddada cewa kada wata kungiya ta sami damar fadawa PDP wanda zai gabatar a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce:

"Atiku shine dan takarar siyasa da ya fi shiri da gogewa a Najeriya don tunkarar jam'iyyar APC."

Fabiyi ya ce hujjar cewa ya kamata a soke Atiku bisa dalilan cewa ya tsufa da yin takara kuma PDP ba ta ci nasara a 2019 ba saboda tsohon mataimakin shugaban kasa ba ya da farin jini a wurin ‘yan Najeriya,“rashin hankali ne.”

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

Ya ce Atiku ne kadai dan siyasa da ya shirya don ceto kasar daga matsaloli daban-daban ciki har da yanayin tattalin arziki da rashin tsaro.

A cewarsa, shugabannin APC sun rasa dabarar da ake bukata don kai kasar zuwa matakin da ake so.

2023: Kada ku bari Atiku ya yi maku asarar tikitinku, kungiya ta gargadi PDP

A wani labari, magoya bayan jam'iyyar Peoples Democratic Party, a karkashin inuwar PDP Action 2023, sun yi kira ga jam'iyyar da ta guji maimaita kuskuren asarar tikitin takarar Shugaban kasa kan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Kungiyar ta yi wannan roko ne a cikin wata sanarwa mai taken, “Kada Atiku Ya sake Bata tikitin PDP” wanda Shugabanta na kasa, Dakta Rufus Omeire, ya sanya wa hannu a Abuja, a ranar Laraba, jaridar.

Kungiyar ta kara gargadin tsohon mataimakin shugaban kasar da kada ya yaudari mambobin jam'iyyar a karo na biyu, jaridar Thisday ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Kada ku bari Atiku ya yi maku asarar tikitinku, kungiya ta gargadi PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel