Gaskiya Ta Fito, An Ji Dalilin Atiku na ƙin Zabar Abokin Takara daga Kudu maso Gabas

Gaskiya Ta Fito, An Ji Dalilin Atiku na ƙin Zabar Abokin Takara daga Kudu maso Gabas

  • Kenneth Okonkwo ya musanta rahotannin cewa ya yi adawa da zaben Rotimi Amaechi a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar a jam'iyyar ADC
  • Okonkwo ya ce matsayinsa shi ne mataimakin shugaban ƙasa ya fito daga Kudu maso Gabas, amma dokar zaɓe ta 2026 ta kawo matsala ga hakan
  • Tsohon kakakin Peter Obi ya sake zargin tsohon ubangidansa da cin amanarsa, yana mai cewa Atiku ya yaba da ƙimarsa duk da sukar da ya riƙa yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

AbujaKenneth Okonkwo, mai magana da yawun ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya yi magana game da Rotimi Amaechi.

Kakakin kungiyar yakin neman Atikun, ya karyata rahotannin da ke cewa ya yi adawa da zaɓen tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takarar Wazirin Adamawa.

Kara karanta wannan

"Obi ya ci amana ta," Sabon mai magana da yawun Atiku ya tada hazo ana shirin zabe

Kenneth Okonkwo ya fadi dalilin da ya sanya Atiku bai zabi abokin takara daga Kudu maso Gabas ba
Atiku Abubakar tare da abokin takararsa a zaben 2027, Rotimi Amaechi. Hoto: @atiku
Source: Twitter

Abin da Kenneth Okonkwo ya ce kan Amaechi

Okonkwo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV a ranar Alhamis.

Da aka tambaye shi ko har yanzu yana adawa da zaɓar Amaechi da aka yi a matsayin abokin takarar Atiku, Okonkwo ya ce babu inda ya taɓa yin irin wannan magana.

Okonkwo ya ce:

"Ban san daga ina aka samo wannan ba."

Ya ƙara da cewa Amaechi shi ne zaɓin ADC, kuma duk wani ɗan jam'iyya na gari ya kamata ya mara masa baya.

Magana kan shiyyar abokin takarar Atiku

Okonkwo ya bayyana cewa abin da ya taɓa faɗa shi ne yana son mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito daga yankin Kudu maso Gabas, amma ba wai yana adawa da Amaechi ba.

A cewarsa, dokar zaɓe ta 2026 ta tanadi cewa duk mai son tsayawa takara dole ne ya kasance ɗan jam'iyya aƙalla kwanaki 21 kafin zaɓen fitar da gwani.

Kara karanta wannan

Atiku ya karfafa shirin kifar da Tinubu, ya nada sabon mai magana da yawunsa

Ya ce hakan ya sa mutanen Kudu maso Gabas da yake ganin sun dace ba su cancanci shiga takarar ba.

Okonkwo ya bayyana cewa kafin zaɓen fitar da gwani, manyan masu neman tikitin shugaban ƙasa sun haɗa da Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, Hayatu-deen da Peter Obi.

Ya ce bayan Peter Obi ya fice daga jam'iyyar, yankin Kudu maso Gabas ya shiga rudani, lamarin da ya takaita zaɓin wanda zai zama mataimakin ɗan takara, in ji rahoton Punch.

Kenneth Okonkwo ya ce Atiku ya ga amfaninsa har ya bashi mukami duk da ya soke shi a baya
Kenneth Okonkwo, sabon mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar. Hoto: Aninze Ekene
Source: Twitter

Ya sake zargin Peter Obi

A wani labari, mun ruwaito cewa, Kenneth Okonkwo, sabon mai magana da yawun Atiku Abubakar ya kuma sake zargin tsohon ubangidansa, Peter Obi, da cin amanarsa.

Ya ce ya daina yi wa Obi aiki tun shekarar 2024 bayan ya yanke hukuncin cewa tsohon gwamnan na Anambra ba shi da jajircewar da ake buƙata domin jagorantar Najeriya.

Sai dai ya ce duk da irin sukar da ya riƙa yi wa Atiku Abubakar a baya, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fahimci ƙimarsa kuma ya ga zai iya ba da gudunmawa wajen gina Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com