Attajiri Lamba 1 a Duniya, Elon Musk Ya Tafka Asarar Dala Biliyan 51 a Awa 24
- Elon Musk ya yi asarar fiye da dala biliyan 51 bayan hannayen jarin SpaceX da Tesla sun fadi a kasuwar hada-hadar hannayen jari ranar Talata
- Duk da asarar da ya yi Musk na ci gaba da zama mutum mafi arziki a duniya gaban wadanda suka kafa kamfanin Google
- Masana sun ce SpaceX na da kyakkyawar makoma duk da saukar darajar hannun jarinta bayan shiga kasuwar hannayen jari kwanan nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Shugaban kamfanonin Tesla da SpaceX, Elon Musk, ya yi asarar fiye da dala biliyan 51 a ranar Talata bayan da darajar hannayen jarin SpaceX da Tesla ta ragu a kasuwar hada-hadar hannayen jari.
Rahoton mujallar Forbes ya bayyana cewa hannun jarin SpaceX ya sauka da sama da kashi shida cikin 100 zuwa kusan $150 a ranar Talata, yayin da na Tesla ya ragu da kusan kashi hudu cikin 100.

Source: Getty Images
Dukiyar Elon Musk ta ragu da $51bn
A cewar rahoton Forbes, wannan sauyi ya rage arzikin Musk da dala biliyan 51.4, inda jimillar dukiyarsa ta sauka zuwa kusan dala biliyan 948.
Mujallar ta ce Musk na da hannayen jari biliyan 4.8 a SpaceX tare da zabin sayen wasu hannaye miliyan 350, baya ga kusan hannaye miliyan 700 da yake da su a Tesla.
Duk da wannan koma baya, wasu manyan bankunan Wall Street sun nuna cewa har yanzu suna da yakinin SpaceX na da kyakkyawar makoma a nan gaba.
Wani masani kan harkokin kasuwanci ya bayyana cewa tasirin da SpaceX za ta iya yi a duniya ya fi na yawancin kamfanonin da suka taba bibiya.
Elon Musk ya mallaki dala tiriliyan
SpaceX ta shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari a watan da ya gabata cikin daya daga manyan abubuwan da aka fi jira a kasuwannin duniya.
A lokacin, arzikin Musk ya kai dala tiriliyan 1.45, lamarin da ya sa ya zama mutum na farko a duniya da dukiyarsa ta haura tiriliyan guda.
Sai dai tun bayan fara cinikin hannun jarin kamfanin, farashinsa na ci gaba da sauyawa sosai, abin da ya janyo Musk ya rika yin asarar daruruwan biliyoyin daloli a lokuta daban-daban.

Source: Getty Images
Elon Musk ne mai kudin duniya
Rahoton ya danganta daya daga cikin manyan faduwar darajar hannun jarin da aka samu a karshen watan Yuni da sayen kamfanin Cursor, mai fasahar kirkirar lambar kwamfuta ta AI, kan dala biliyan 60, matakin da wasu masana suka ce zai iya rage darajar hannayen masu zuba jari.
Duk da haka, Elon Musk na ci gaba da kasancewa mutum mafi arziki a duniya da tazara mai yawa, inda ya zarce wadanda suka kafa Google, Larry Page da Sergey Brin, da ke matsayi na biyu da na uku a jerin masu kudin duniya.
Musk ya kafa ko kuma ya taimaka wajen kafa kamfanoni bakwai, ciki har da Tesla, SpaceX, xAI, The Boring Company da Neuralink, wadanda ke daga cikin manyan hanyoyin da suka gina masa wannan dimbin arziki.
Asali: Legit.ng

