Matar Tinubu Ta Koma Gona, Ta Girbe Abubuwan da Ta Shuka da Kanta
- Rahotanni sun nuna cewa uwargidan shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu ta sake girbe kayan lambu daga gonarta da ke Aso Rock Villa a Abuja
- Sanata Remi Tinubu ta buƙaci 'yan Najeriya su rungumi noma a cikin gida domin bunkasa samar da abinci da habaka tattalin arzikin al'umma
- Matar shugaban kasar ta bayyana cewa yin noma a cikin gida na rage kuɗin da maza ke kashewa tare da samar da lafiyayyen abinci ga iyalansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta sake girbe kayan lambu daga gonarta da ke fadar shugaban kasa.
Rahotanni sun nuna cewa an yi gonar ne kimanin shekaru biyu da suka gabata domin inganta samar da wadataccen abinci a Najeriya ta hanyar shirin samar da abinci a gidaje.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai game da girbin da Sanata Remi Tinubu ta yi ne a wani sako da tashar NTA ta wallafa a shafinta na Facebook.
Kiran Remi Tinubu kan noma
Bayan ziyarar da ta kai gonar domin wani sabon girbi, uwargidan shugaban kasar ta sake kira ga 'yan Najeriya da su rungumi noman gida domin ƙarfafa samar da abinci da kuma tabbatar da wadatar abinci a ƙasa.
Ta nuna amfanin gonar da ta girba, ciki har da alayyahu, rama da ugu, tana mai cewa noman gida hanya ce mai sauƙi kuma mai araha ta samun lafiyayyen abinci.
A hotunan da tashar TVC ta wallafa, an hango matar shugaban kasar da wasu mutane a gonar suna rike da kayan lambu a ciki leda.
An hango Remi Tinubu da kanta tana yanke kayan lambu a wajen da ta yi shuka, lamarin da ke nuna tana aikin gonar da kanta.

Kara karanta wannan
Tinubu ya waiwayi manyan kamfanonin kafafen sadarwa, za a binciki Meta, X da sauransu
Amfanin noma inji Remi Tinubu
Matar shugaban kasar ta kuma bayyana cewa baya ga tabbatar da wadatar abinci, noman gida na taimakawa wajen yaƙi da sauyin yanayi.
Oluremi Tinubu ta raba wani ɓangare na amfanin gonar da ma'aikatanta, tare da tunatar da 'yan Najeriya muhimmancin tausayi da kyauta ga mutane.
Ta ƙara da cewa noman gida na taimaka wa iyalai wajen rage kuɗin cefane, samun sababbin kayan lambu masu gina jiki, da kuma ƙarfafa dogaro da kai wajen samar da abinci.
Sanata Remi Tinubu da ta shafe lokaci tana kira ga mutane da su rika noma a gida domin taimakawa iyalansu, inda ta bukaci kowane gida ya samar da lambu.

Source: Facebook
Remi Tinubu ta karfafi mata
A wani rahoton, mun kawo muku cewa matar shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu ta karfafi mata kan rike kananan sana'o'i gam ba tare da raina su ba.
Ta bayyana haka ne yayin da ta je wani taro na musamman jihar Kaduna, inda ta ce riko da kananan sana'o'i na da matukar muhimmanci.
Remi Tinubu ta yi kiran ne a daldai lokacin da ake caccakar ta bayan ta ce suna ba da tallafi ga masu gasa masara da tuyan kosai.
Asali: Legit.ng
