Gwamnoni 18 da ke Neman Tazarce a Zaben 2027 Sun Yi Ganawar Sirri a Kebbi, An Samu Bayani

Gwamnoni 18 da ke Neman Tazarce a Zaben 2027 Sun Yi Ganawar Sirri a Kebbi, An Samu Bayani

  • Gwamnonin jam'iyyar APC 18 da ke wa'adin farko a kan mulki sun shiga wata ganawar sirri a gidan gwammatin jihar Kebbi
  • Gwamna Nasir Idris na Kebbi ne ya karɓi baƙuncin taron wanda rahotanni suka nuna yana ci gaba da gudana yanzu haka a Birnin Kebbi
  • Bayanai sun nuna cewa gwamnonin APC biyu ba su samu halartar taron amma amma sun aika da sakon neman uzuri da kuma bada hakuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Birnin Kebbi, Nigeria - Gwamnoni 18 na jam'iyyar APC da ke wa'adin farko a kan karagar mulki sun shiga wani taron gaggawa a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnonin, wadanda ke shirin neman wa'adi na biyu a zaben 2027 da ke tafe, sun shiga taron ne a fadar gwamnatin Kebbi yau Talata, 7 g watan Yuli, 226.

Kara karanta wannan

Gwamna Alia ya bugi kirji, ya fadawa Tinubu yawan kuri'un da zai samu a Benue

Gwamna Nasir Idris.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idrishana jawabi a taron majalisar zartarwa a Birnin Kebbi Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Gwamna Nasir ya karɓi baƙuncin taron

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris wanda yana daya daga cikin gwamnonin da ke wa'adin farko, shi ne ya karɓi baƙuncin taron.

Taron ya samu halartar galibin gwamnonin APC da ke wa’adin farko daga jihohi daban-daban na ƙasar domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jam’iyyar da kuma harkokin mulkin ƙasa.

Jihohin da suka halarci taron

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai na jihohin Sokoto, Kaduna, Jigawa, Plateau, Delta, Ekiti, Taraba, Ondo, Ebonyi, Akwa Ibom, Edo, Benue, Kogi da Enugu, tare da sauran jihohin da APC ke mulki.

Sai dai gwamnonin jihohin Cross River, Niger da Katsina ba su samu halartar taron ba, bayan sun aika da saƙon neman afuwa kan rashin halartarsu.

Abubuwan da gwamnonin suka cimma

Bayan kammala taron, gwamnonin sun jadada cikakken goyon bayansu ga sauye-sauyen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da kuma hunkurinsa na neman tazsrce a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Manyan masu ruwa da tsaki a Gombe sun ɗauki wanda suke so ya zama gwamna a 2027

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya wallafa a shafinsa na Facebook jim kadan bayan fitowa daga taron.

Gwamnonin APC.
Gwamnonin APC da ke wa'adi na farko bayan taron da suka gudanar a jihar Kebbi Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook
"Mun jaddada goyon bayanmu ga sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, tare da tabbatar da aniyarmu na ganin Ajandar Renewed Hope ta ci gaba har bayan 2027.
"Mun fahimci irin sadaukarwa da kuma haƙurin da ‘yan Najeriya ke yi a wannan lokaci, amma muna da yakinin cewa waɗannan sauye-sauye na kafa tubalin gina ƙasa mai ƙarfi, mai wadata da kuma ingantaccen tsaro."

- Gwamna Nasir Idris.

Gwamna Nasir ya yiwa Tinubu alƙawari

Kun ji cewa Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa Kebbi tana tare da Bola Tinubu, yana mai danganta hakan da ayyukan ci gaba da aka aiwatar cikin shekaru uku da suka gabata.

Gwamnn ya tabbatar wa shugaban kasa mutanen jihar Kebbi za su maida biki ta hanyar sale kada masa kuri'u saboda ayyukan da ya musu.

Ya fadi haka ne a wurin wani gangami da APC ta shirya a jihar Kebbi domkn tabbatar da goyon bayanta ga tazarcen Shugaba Tinubu a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262