Tsohon Sakataren Gwamnati Tare da Wasu Mutum 50,000 Sun Fice Daga APC, Sun Koma PDP
- Wasu mambobin jam'iyyar APC sama da 50,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Adamawa
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yace an yafe musu zunubansu na zama a jam'iyyar da ta gaza da farko
- Gwamnan Adamawa ya roki sabbin yan PDP da su nuna goyon bayansu ga takatar Atiku a babban zaɓen dake tafe
Adamawa - Sama da mutum 50,000 mambobin jam'iyyar APC, tare da tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, Mr Kobis Ari Themnu, sun sauya sheka zuwa PDP, kamar yadda leadership ta ruwaito.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, shine ya tarbe su a babban filin taro na Ribaɗu Square, jihar Adamawa.
Atiku ya nuna matukar rashin jin dadinsa bisa yadda masu sauya shekar suka yi ɗa'a ga jam'iyyar da ta gaza a baya.
Sai dai yace a halin yanzun an yafe musu kasancewarsu da APC a baya, kuma ya tabbatar musu da cewa PDP ta ƙagu ta kwace mulki a zaɓen 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Atiku, wanda ya sha kaye a hannun shugaba Buhari a zaɓen 2019, ya roki sauran mambobin jam'iyyu su shigo PDP domin kawo cigaba a jihar da ƙasa baki ɗaya.
Shin Atiku ya fara kamfe kenan?
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Ahmadu Fintiri, yace ba za'a nuna banbanci ba tsakanin waɗanda suka sauya sheka da kuma yan jam'iyyar PDP na asali.
Gwamnan ya sha alwashin yin adalci a gangamin tarukan PDP dake tafe reshen jihar, kuma kowa zai iya neman mukamin da yake so.
Ya kuma roki sabbin mambobin su shigo a mara wa kudirin Atiku Abubakar baya na sake neman ɗarewa mulkin Najeriya a babban zaɓen 2023 dake tafe.
Kofar PDP a buɗe take ga kowa
A nasa ɓangaren, shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Adamawa, Barista Tahir Shehu, yace wannan taron somin taɓi ne na waɗanda zasu shigo PDP daga sauran jam'iyyun siyasa.
A cewarsa jam'iyyar PDP ta ɗauki ɗamarar samar da shugaban ƙasa daga yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Barista yace:
"Kofar mu a buɗe take ga duk wanda yake sha'awar shigowa jam'iyyar PDP a tafi tare. Cigaban da wannan gwamnatin ta kawo kaɗai ya isa nuna mana siyasar da ta dace mu yi a jihar mu gabanin 2023."
"Zamu haɗa karfi-da-karfe tare da sabbin mambobin PDP da suka shigo domin nasarar jam'iyyar mu nan gaba."
Rikicin PDP a zaɓen gwamnan Anambra
A wani labarin kuma Kotu Ta Bayyana Valentine a Matsayin Dan Takarar PDP a Zaben Gwamna Dake Tafe
Kotun ɗaukaka kara ta Awka ta tabbatar da cewa Valentine Ozigbo, shine halastaccen ɗan takarar gwamnan Anambra a zaɓen dake tafe karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki
Kotun tace jam'iyyar PDP ta cika ka'idoji wajen gudanar da zaɓen fidda gwani, wanda ya baiwa Ozigbo damar zama ɗan takararta, kamar yadda punch ta ruwaito.
Ta kuma umarci hukumar zabe INEC ta saka sunan Ozigbo da abokin takararsa cikin waɗanda zasu fafata a watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng