Bayani Daki Daki: Yadda Ƴan Najeriya Za Su Sabunta Fasfo ba Tare da zuwa Ofis ba

Bayani Daki Daki: Yadda Ƴan Najeriya Za Su Sabunta Fasfo ba Tare da zuwa Ofis ba

  • Hukumar NIS ta fitar da sabon tsarin sabunta fasfo ga 'yan Najeriya mazauna kasashen waje ta hanyar kai-da-kai ba tare da zuwa ofishin jakadanci ba
  • Sabon tsarin ya bai wa masu cancanta damar yin rajistar bayanan tantance su ta manhajar da hukumar ta samar, kuma za su hakan cikin sauki
  • Hukumar ta ce wadanda ba su cancanci amfani da tsarin ba ne kawai za su ci gaba da yin rajistar ganawar kai tsaye a ofisoshin jakadancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya (NIS) ta fitar da sabon tsari da aka kawo na yadda 'yan Najeriya mazauna kasashen waje za su sabunta fasfo dinsu.

A wannan tsarin, 'yan Najeriya mazauna waje za su iya sabunta fasfo ta hanyar sabon tsarin samun fasfo ta kai-da-kai, ba tare da mutum ya je ofishin jakadanci ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya waiwayi manyan kamfanonin kafafen sadarwa, za a binciki Meta, X da sauransu

Hukumar NIS ta samar da sabon tsarin sabunta fasfo ga 'yan Najeriya mazauna waje.
Fasfon 'yan Najeriya karkashin ECOWAS da kuma shugabar hukumar NIS, CGI KN Nandap. Hoto: @nigimmigration/X, Getty Images.
Source: Twitter

NIS ta kawo sabon tsarin sabunta fasfo

Hukumar ta sanar da hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X ranar Talata, inda ta bukaci 'yan Najeriya da ke zaune a ketare su yi amfani da wannan dandali na zamani wajen sabunta fasfo ba tare da sun sha wahala ba.

A cewar NIS, mai neman sabunta fasfo zai fara shiga shafin neman fasfo na hukumar, sannan ya zabi 'Apply for Renewal/Re-issue'.

Daga nan zai kirkiri asusu tare da tabbatar da bayanansa ta amfani da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) da ranar haihuwa.

Bayan haka, mai nema zai cike fom din neman fasfo, ya zabi karami ko babban ofishin jakadancin da yake son a kammala aikinsa, sannan ya dora takardun da ake bukata tare da biyan kudin fasfo.

Yadda za a sabunta fasfo cikin sauki

Da zarar ya samu Application ID da Reference Number, zai zabi tsarin Contactless (ma'ana ba sai ya je ofis ba), ya amince da sharuddan amfani da shi, sannan ya sauke manhajar hukumar NIS.

Kara karanta wannan

A yi hattara: Katsina, Sokoto da wasu jihohi 25 za su fuskanci ambaliyar ruwa

Ta cikin manhajar ne zai shiga asusunsa, ya zabi ayyukan da suka shafi fasfo (Passport Application Services), sannan ya yi rajistar hoton fuskarsa da yatsun hannunsa tare da kammala tantancewar mutum. Bayan haka zai biya kudin sabis din tsarin kai-dakai kafin ya mika bayanan yatsu da fuskarsa.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa ba duk masu neman fasfo ne za su cancanci amfani da wannan tsarin ba.

Ta ce idan sakamakon tantancewar ya nuna 'baka cancanta ba', to dole ne mai neman fasfo ya koma shafin farko na tsarin domin yin rajistar ganawar kai tsaye a ofishin jakadancin Najeriya ko babban ofishin jakadancin da ya zaba.

Hukumar NIP ta yi nuni da cewa za a iya samun wadanda ba za su amfana da wannan tsarin na kai-da-kai ba.
Shugabar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, KN Nandap a wajen wani taro. Hoto: @nigimmigration
Source: Twitter

Karin bayani ga masu sabunta fasfo

Ga wadanda suka kammala rajistar tantance kansu cikin nasara, NIS ta ce wajibi ne su buga fom din neman fasfo, shaidar biyan kudin fasfo, shaidar biyan kudin shigar da bayanan fuska da yatsu da kuma kwafin fasfonsu na yanzu.

Dole ne a hada wadannan takardu a cikin ambulan da aka rubuta adireshin mai nema sannan a aika su zuwa ofishin jakadancin da aka zaba yayin cike fom din.

Hukumar ta kara da cewa bayan kammala aikace-aikacen, masu neman fasfo za su iya bibiyar ci gaban bukatarsu bayan makonni biyu ta hanyar shafin bin diddigin NIS ko kuma manhajar NIS.

Kara karanta wannan

Komai zai fito: APC na shirin fitar da bayanan mataimakin Tinubu a 2027

Najeriya ta kara kudin fasfo

A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar shige da fice ta kasa ta fitar da sanarwa kan karin kudin fasfo da zai ba yan Najeriya damar fita kasashen ketare.

Hukumar shige da fice ta kasa ta tabbatar da cewa an samu karin kudin ne domin inganta fasfo din Najeriya a idon duniya.

Haka zalika hukumar NIS ta bayyana cewa a farkon watan Satumba mai zuwa yan Najeriya za su fara biyan sabon farashin fasfon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com