An Saki Bama Bamai yayin da Shugaban Faransa Ya Isa Kasar Syria
- Fashewar bam-bamai biyu ta girgiza Damascus yayin da shugaban Faransa, Emmanuel Macron ke ziyarar aiki a kasar Syria
- An rahoto cewa aƙalla mutum 18 sun jikkata, ciki har da jami’an ‘yan sanda huɗu, sai dai babu labarin mutuwa a wajen
- Shugaba Macron na ziyara a Syria ne domin ƙarfafa dangantaka da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyoyin tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Syria - Fashewar bam-bamai ta girgiza birnin Damascus a ranar Talata yayin da shugaban Faransa, Emmanuel Macron ke ganawa da takwaransa na Syria, Ahmad al-Sharaa.
Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutum 18 suka jikkata, kamar yadda ma’aikatar harkokin cikin gida ta Syria ta bayyana.

Source: Getty Images
Kafar yada labarai ta AP ta ce Macron ya shiga fadar shugaban ƙasa domin ganawa da shugaba Ahmad al-Sharaa a lokacin da fashewar ta afku.
Wajen da bam ya tashi a Syria
Hotunan da suka bazu a kafafen sada zumunta sun nuna wata mota daukar kaya da babur suna ci da wuta, tare da tabon jini a kan titi.
Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan fashewar wata na’urar bama-bamai a wani gidan shan shayi kusa da kotu a Damascus, wanda ya kashe aƙalla mutum 10 tare da jikkata sama da mutum 20.
Duk da cewa sabuwar gwamnatin Syria na ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula daga ƙungiyoyi daban-daban yayin da take ƙoƙarin tabbatar da cikakken iko a ƙasar, babban birnin Damascus ya kasance cikin kwanciyar hankali sosai.
Yaƙin Syria ya yi sanadin mutuwar kusan mutum rabin miliyan tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu kuma abubuwan more rayuwa na ƙasar sun lalace.
Macron yana cikin ƙoshin lafiya
Wata majiya ta tsaro ta shaida wa BBC cewa fashewar ta samo asali ne daga na’urori biyu masu fashewa. Kafafen yaɗa labaran Syria sun ce mutum 18, ciki har da jami’an ‘yan sanda huɗu, sun jikkata.
Macron yana Damascus ne domin tattaunawa da shugaban Syria, Ahmad al-Sharaa a fadar shugaban ƙasa. Jami’ansa sun tabbatar da cewa yana cikin ƙoshin lafiya kuma bai ji fashewar ba.
Gwamnatin Syria ta bayyana cewa an boye ɗaya daga cikin bama-baman a kwandon shara, ɗaya kuma a cikin wata mota da aka ajiye.

Source: Getty Images
Ta ƙara da cewa huɗu daga cikin waɗanda suka jikkata jami’an ‘yan sanda ne, kuma babu rahoton mutuwa, inda ta ce ana ci gaba da bincike a wurin da lamarin ya faru.
An ga wani babban hayaƙi yana tashi daga wurin da abin ya faru. Yankin na kan wata babbar hanya ce mai cunkoson jama'a a Damascus, kusa da hedikwatar ma’aikatar yawon buɗe ido da kuma gidan tarihi na kasa na Damascus.
An saki bama-bamai a Ukraine
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya kaddamar da manyan hare-hare a babban birnin Ukraine.
An bayyana cewa hare-haren sun ruguza gine-gine da dama, jikkata jama'ar da ke kusa da wuraren da ka kai hari tare da jawo asarar rayuka.
Ukraine ta yi Allah wadai da hare-haren, inda ta bukaci Amurka da kasashen Turai su gaggauta kawo mata dauki domin dakile barnar da Putin ke mata.
Asali: Legit.ng

