Kotu Ta Bayyana Valentine a Matsayin Dan Takarar PDP a Zaben Gwamna Dake Tafe

Kotu Ta Bayyana Valentine a Matsayin Dan Takarar PDP a Zaben Gwamna Dake Tafe

  • Kotun daukaka kara ta tabbatar da Valentine Ozigbo, a matsayin ɗan takarar PDP a zaɓen gwamnan Anambra
  • Kotun tace jam'iyyar PDP ta cika ka'idoji wajen gudanar da zaɓen fidda gwani, wanda ya baiwa Ozigbo damar zama ɗan takararta
  • Ta kuma umarci hukumar zabe INEC ta saka sunan Ozigbo da abokin takararsa cikin waɗanda zasu fafata a watan Nuwamba

Anambra - Kotun ɗaukaka kara ta Awka ta tabbatar da cewa Valentine Ozigbo, shine halastaccen ɗan takarar gwamnan Anambra a zaɓen dake tafe karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

A hukuncin da kotun ta yanke ranar Jumu'a, karkashin jagorancin mai Shari'a Monica Dogban Mensem, tace zaɓen fidda gwani da jam'iyyar PDP ta gudanar, wannda Ozigbo ya zama zaɓaɓɓen ɗan takara halastacce ne.

Hakanan kuma Kotun ɗaukaka karar ta jingine hukuncin da kotu ta yanke kan lamarin a baya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina

Valentine Ozigbo
Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Bayyana Valentine a Matsayin Dan Takarar Gwamna a Karkashin PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta gano cewa a ranar 6 ga watan Nuwamban dake tafe za'a gudanar da zaɓen gwamna a jihar Anambra.

Kotu ta umarci INEC ta saka sunan Ozigbo

Channels tv ta ruwaito cewa kotun ta umarci hukumar zaɓe INEC, ta saka sunan Ozigbo da abokin takararsa a cikin jerin sunayen yan takarar da zasu fafata a zaɓen gwamnan dake tafe.

Bugu da kari ta roki INEC ta daina saka kanta a cikin rikita-rikatar dake faruwa a cikin babbar jam'iyyar hamayya PDP.

Ta kuma shawarci hukumar da ta rinka jiran hukuncin babbar kotu na karshe kafin ta yi saurin yin ɗa'a ga hukuncin karamar kotu.

Shin INEC ta cire sunan Ozigbo?

A watan Yulin da ya gabata, INEC ta cire sunan Ozigbo daga jerin sunayen yan takarar da zasu fafata a zaɓen gwamnan, domin yin biyayya ga hukuncin kotu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar ta baci, ta kulle dukkan makarantun jihar

Amma da yake martani kan cire sunansa da INEC ta yi, Ozigbo ya bayyana cewa, "Matakin INEC na wani lokaci ne."

Yace jam'iyyar PDP ta shirya lauyoyi da duk abinda suke bukata domin tabbatar da an soke hukuncin kotun, wanda zai baiwa INEC damar maida sunansa a cikin yan takara.

Mista Ozigbo ya jaddada cewa sunan shi kaɗai jam'iyyar PDP ta aike wa hukumar zaɓe a matsayin ɗan takara a zaɓen gwamna dake tafe.

A wani labarin kuma Gwarazan Yan Sanda Sun Ceto Mutum 8 da Yan Bindiga Suka Sace a Zamfara

Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta samu nasarar ceto wasu mutum 8 da yan bindiga suka sace a Bungudu.

Kakakin yan sandan jihar, ASP Muhammad Shehu, yace an samu wannan nasarar ne cikin ruwan sanyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262