Sakamakon Zabe: APC Ta Lashe Kananan Hukumomi 8, PDP Ta Ci Daya a Jihar Kaduna

Sakamakon Zabe: APC Ta Lashe Kananan Hukumomi 8, PDP Ta Ci Daya a Jihar Kaduna

  • Bayan kammala zaben kananan hukumomi a jihar Kaduna, sakamako ya fara fitowa daga bakin baturen zabe
  • Rahoto ya nuna cewa an gudanar da zaɓe a kananan hukumomi 19 cikin 23 dake jihar
  • A halin yanzun, jam'iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki ta lashe 8 yayin da PDP ta samu ɗaya tal

Kaduna - Sakamakon zaɓen kananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar a jihar Kaduna ya fara hitowa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta gano cewa an gudanar da zaɓen a kananan hukumomi 19 cikin 23 dake jihar Kaduna.

Daga cikin kananan hukumomi 9 da aka bayyana sakamakonsu zuwa yanzun, APC ta lashe 8 yayin da babbar abokiyar hamayyarta PDP ta samu ɗaya.

Malamin zabe yayin gudanar da aiki a runfar zaɓe
Sakamakon Zabe: APC Ta Lashe Kananan Hukumomi 8, PDP Ta Ci Daya a Jihar Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ga yadda sakamakon yake fitowa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Lallasa El-Rufa'i da APC a Zaɓen Kansila Na Gundumar Gwamnan Kaduna

Karamar hukumar Kubau

Baturen zaɓen karamar hukumar Kubau, Mallam Dayyabu Muhammed, ya sanar da Bashir Zuntu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Baturen zaɓen yace ɗan takarar na APC ya samu kuri'u 23,973, wanda ya bashi damar Lallasa abokan takararsa na PDP, Malam Isa Rabiu Imam, mai kuri'u 9,038.

Kudan

Mista Haruna Abdu, baturen zaɓen karamar hukumar Kudan, ya bayyana Alhaji Shu'aibu Jaja, na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓe da kuri'u 18,129.

Jaja ya samu nasarar doke Ibrahim Shehu Doka, na jam'iyyar PDP, wanda ya samu kuri'u 16,123 da Umar Taba na Labour Party, wanda ya samu kuri'u 1,844.

Lere

A karamar hukumar Lere, Alhaji Abubakar Buba, na jam'iyyar APC, shine ya samu nasara da kuri'u 36,389, inda ya doke Dalhat Abu-Dadda’i na jam'iyyar PDP, wanda ya samu kuri'u 24,294.

Zaria

Hakazalika, Alhaji Idris Ibrahim, na jam'iyyar APC ya lashe kujerar shugaban ƙaramar hukumar Zaria da kuri'u 34,006.

Kara karanta wannan

Zaben Kananan Hukumomi: Yan Daba Sun Sace Na'urar Zaɓe Sama da 40 a Kaduna, El-Rufa'i Ya Magantu

Inda ya lallasa babban abokin takararsa na jam'iyyar PDP, Alhaji Yusuf Sambo, wanda ya samu kuri'u 14,019 dai-dai.

Sabon Gari

Alhaji Mohammed Usman, na jam'iyyar APC shine ya lashe zaɓen karamar hukumar Sabon Gari da kuri'u 32,405, ya doke Alhaji Abdu Bello na PDP mai kuri'u 13,777.

Jema'a

Yunana Markus Barde na jam'iyyar APC ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙaramar hukumar Jema'a da kuri'u 24,255.

Wannan nasarar ta sa APC ta doke shugaban da ya gabata na jam'iyyar PDP, Peter Danjuma Averik, wanda ya sami kuri'u 23,215.

Baturen zaɓen Sanga, Dakta Sunday Ibrahim, shine ya sanar da sakamakon bayan kammala tattarawa.

Kaura

Baturen zaɓen Kaura, Farfesa Katoh Ishaya, ya sanar da ɗan takarar PDP, Matthias Siman, a matsayin wanda ya lashe zaɓen ƙaramar hukumar da kuri'u 19,511.

Siman ya lallasa babban abokin takararsa na jam'iyyar APC, Adamu Donatus, wanda ya samu kuri'u 10,941.

Sanga

Da yake sanar da sakamakon zaɓen, baturen zaben karamar hukumar yace ɗan takarar APC, Bisallah Malam, ya samu kuri'u 21,854, inda ya samu nasara a kan abokin takararsa na PDP da ya samu kuri'u 12,832.

Kara karanta wannan

Zaben kananan hukumomin Kaduna: PDP ta lallasa APC a akwatin mazabar Gwamna El-Rufa'i

Kagarko

Baturen zaɓe, Dakta Musa Balarabe Makarfi, ya bayyana ɗan takarar APC, Hon. Nasara Rabo, a matsayin wanda ya lashe zaɓen karamar hukumar Kagarko da kuri'u 20,558.

Rabo ya doke abokin takararsa na jam'iyyar PDP, Caleb Pius, wanda ya samu kuri'u 14,494.

A wani labarin kuma Bayan Ganawa da Shugaba Buhari, Sanatan Ndume Ya Sake Magana Kan Mayakan Boko Haram da Suka Mika Wuya

Sanata Ali Ndume, na jam'iyyar APC, yace har yanzun yana kan maganarsa ta farko cewa a gurfanar da tubabbun yan Boko Haram.

Sanatan ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja jim kaɗan bayan ganawa da Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel