Zaka Zubar da Mutuncinka Matukar Ka Sauya Sheka Zuwa APC, Jigon PDP Ya Faɗawa Jonathan

Zaka Zubar da Mutuncinka Matukar Ka Sauya Sheka Zuwa APC, Jigon PDP Ya Faɗawa Jonathan

  • Jigon babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP ya gargaɗi Jonathan kan shirin komawa APC mai mulki
  • Dr Okwesilieze Nwodo, wanda tsohon shugaban PDP ne yace zai matukar bakin ciki idan Jonathan ya sauya sheka
  • Yace da zarar tsohon shugaban ya koma APC duk wata ƙima da mutuncinsa zai zube a idon yan Najeriya

Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dr Okwesilieze Nwodo, ya gargaɗi tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan kada yayi gangancin komawa jam'iyya mai mulki APC, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Nwodo ya bayyana cewa matukar Jonathan ya koma APC to ya zubar da ragowar mutuncinsa da kimarsa a idon yan Najeriya.

Yace tsohon shugaban ba zai iya kawo sauyi a jam'iyyar ba domin komawarsa zata ƙara shagwaba yan APC ne su cigaba da ɗaukar abinda duke yi dai dai ne.

Kara karanta wannan

2023: Ainihin abin da ya sa APC ke neman tsaida Jonathan yayi mata takarar Shugaban kasa

Dakta Nwodo ya yi wannan maganar ne yayin da yake zantawa da kafar watsa labarai ta Arise Tv.

Tsohon shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan
Zaka Zubar da Mutuncinka a Idon Yan Najeriya Matukar Ka Sauya Sheka Zuwa APC, Jigon PDP Ya Faɗawa Jonathan Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Duk wanda ya koma APC ya fara dana sani

Jigon jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP ya ƙara da cewa duk wanda ya fice daga PDP ya koma APC kan kowane dalili ya fara dafa keya yana dana sani.

A cewarsa babu wani abun da zaka ji dadi ko kayi murna a jam'iyyar APC kuma yace ba zai ji ɗaɗin ganin Jonathan a APC ba.

Wani sashin jawabinsa yace:

"Shawarata ga Jonathan kada ya kuskura ya afka duk wani daɗin baki da tarairayar da ake masa ya koma APC. Daga ranar da ya shiga APC ya gama zubar da ragowar ƙimarsa."
"Wannan itace shawara ta gareshi domin babu mutanen da suka ci mutuncinsa a matsayinsa na shugaban ƙasa kamar jam'iyyar APC, me zai sa ya shige ta? Shin yana tunanin gyara abinda aka lalata ne idan ya koma APC? Ba zai yuwu ba."

Kara karanta wannan

Kafa jam'iyyar APC shine babban kuskuren da aka taba yi a Najeriya, inji Atiku

Wace jam'iyya ce zata iya ceto Najeriya?

Mista Nwodo ya ce PDP ce kaɗai zata iya zuwa madafun iko ta sassaita komai da APC ta lalata kuma ta ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta yau.

Yace:

"Mutum ɗaya tilo da zai iya zuwa ya ceto Najeriya daga halin ƙaƙanikayi da ta tsinci kanta yau ƙarƙashin APC shine shugaban ƙasa a karkashin PDP."
"Goodluck Jonathan babban abokina ne, mun yi aiki tare, zan yi matukar bakin ciki idan ya sauya sheka zuwa APC, bansan mai zai yi a can ba."

A wani labarin kuma Barayin da Suka Sace 'Ya'ya da Matar Babban Malamin Addini Sun Nemi a Tattaro Musu Miliyan N50

Barayin da suka jagoranci sace matar wani babban malamin addinin kirista a Abuja da ƴaƴansa mata biyu sun nemi fansa

Wata majiya tace maharan sun kira ɗaya daga cikin makusantan waɗanda aka sace ranar Lahadi da karfe 11:00 na dare, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon Sakataren Gwamnati Tare da Wasu Mutum 50,000 Sun Fice Daga APC, Sun Koma PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel