Zaben kananan hukumomin Kaduna: APC ta lallasa PDP, ta lashe kujeru 15 na ciyamomi

Zaben kananan hukumomin Kaduna: APC ta lallasa PDP, ta lashe kujeru 15 na ciyamomi

  • Jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta lallasa PDP a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata
  • Jam'iyyar mai mulki ta kawo kujerun ciyamomi 15 yayin da PDP ta kawo kujeru biyu kawai
  • An dage zabe a kananan hukumomi hudu daga cikin kananan hukumomi 23 na jihar zuwa ranar 25 ga watan Satumba saboda matsalar tsaro

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe mafi yawan kujerun ciyamomi da kansiloli a zabukan kananan hukumomi da aka gudanar a jihar Kaduna a ranar Asabar.

Jam’iyya mai mulki ta lashe kujeru 15 cikin 17 da aka bayyana sakamakon su zuwa yanzu, yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ta lashe sauran biyun, jaridar Premium ta ruwaito.

Zaben kananan hukumomin Kaduna: APC ta lallasa PDP, ta lashe kujeru 15 na ciyamomi
APC ta lallasa PDP a zaben ciyamomi Hoto: The Guardian
Asali: UGC

An dage zabe a kananan hukumomi hudu daga cikin kananan hukumomi 23 na jihar zuwa ranar 25 ga watan Satumba saboda matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

An kuma: PDP ta sake lallasa APC a jihar Kaduna a zaben kananan hukumomi a Jaba

An sha mamaki lokacin da PDP ta yi nasara a mazabar Unguwan Sarki ta Gwamna Nasir El-Rufai a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, APC ta yi gangami don lashe kujerun ciyamomi da mafi akasarin kujerun kansiloli.

Haka kuma APC ta yi nasara a mahaifar manyan jiga-jigan PDP, ciki har da na tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo da tsohon Gwamna Ahmed Makarfi.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Hadiza Balarabe ita ma ta kawo wa APC karamar hukumar Sanga da ke yankin kudancin jihar.

Jam'iyyar PDP ta samu kujerun ciyamomi biyu a kananan hukumomin Jana da Kaura.

Jami'in zaben, Haruna Ahmadu ya bayyana zaben karamar hukumar Kachia a matsayin ba kammalalle ba.

An dage zabe

Za a gudanar da zabukan cikin makwanni uku masu zuwa a kananan hukumomin Birnin Gwari, Chikun, Zangon Kataf, da Kajuru biyo bayan dage zaben saboda dalilan tsaro.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnonin APC 5 da ka iya tsayawa takara a gefen Goodluck Jonathan

Zaɓen ƙananan hukumomi: Nasarar da PDP ta yi a akwati na ya nuna APC bata yi maguɗi ba, El-Rufai

A gefe guda, Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya ce nasarar da jam'iyyar PDP ta samu na lashe zabe a akwatinsa ya nuna cewa APC bata yi maguɗi ba da na'urar zabe na zamani, rahoton The Cable.

A ranar 4 ga watan Satumba, hukumar zabe na jihar Kaduna, KADSIECOM, ta yi zabe ta hanyar amfani da na'urar mai amfani da lankarki.

Kafin wannan lokacin, Jihar Kaduna ce ta farko da ta fara amfani da wannan sabon tsarin zaben na zamani a Nigeria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng