Noma Tushen Arziki: Gwamnatin Tinubu Ta Raba Tallafi ga Dubban Manoma a Gombe

Noma Tushen Arziki: Gwamnatin Tinubu Ta Raba Tallafi ga Dubban Manoma a Gombe

  • Gwamnatin Tarayya ta raba takin zamani da sauran kayan noma ga dubban manoma a jihar Gombe
  • Shirin ya haɗa Bankin Noma da Algir Integrated Services, yana ba manoma kayan noma, kuɗin tallafi da horo
  • Jami'ai sun bukaci manoma su yi amfani da kayan yadda ya dace, suna mai cewa shirin zai taimaka wajen bunƙasa noma da inganta tsaron abinci a Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fara rabon takin zamani da sauran kayan noma ga kananan manoma 5,642 a Gombe.

Gwamnatin tarayya ta ɗauki wannan mataki ne domin tallafa musu a daminar shekarar 2026. Shirin yana ƙarƙashin Asusun Tallafin Manoma Ƙanana da Sarkar Darajar Noma na Renewed Hope.

Gwamnatin Tinubu ta raba kayan tallafin noma
Gwamna Inuwa Yahaya da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Ismaila Uba Misilli.
Source: Facebook

Manufar ba da tallafin noma ga manoma

Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci ta Tarayya ce ke aiwatar da shirin tare da haɗin gwiwar Bankin Noma da kamfanin Algir Integrated, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'Ka tuna kamfen da muka yi maka a baya': Matar El Rufai ta roki Tinubu

Manufarsa ita ce ƙara yawan samar da abinci da sauƙaƙa wa manoma samun ingantattun kayan noma.

Majiyoyi sun ruwaito cewa shirin na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatin tarayya a ƙarƙashin Ajandar Renewed Hope.

Ana kuma ba manoma damar samun kuɗin tallafi, horo kan noma, haɗa amfanin gona da kasuwanni cikin tsari.

An raba kayan tallafin noma a Gombe
Taswirar jihar Gombe da gwamnatin Bola Tinubu ta raba tallafi. Hoto: Legit.
Source: Original

Musabbabin raba kayan tallafin noma

Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Bankin Noma, Ayo Sotinrin, wanda Hajiya Rabi Kabir ta wakilta, ya ce shirin babban mataki ne na rage wa manoman Najeriya nauyin noma su kaɗai.

A saƙon da aka karanta a madadinsa, Sotinrin ya bayyana cewa an tsara shirin ne domin samar da kayan noma, kuɗin tallafi, horo, haɗa amfanin gona da kuma tabbatar da kasuwar sayar da amfanin gonar manoma.

Sotinrin ya bayyana cewa ana sa ran shirin zai kai ga kananan manoma miliyan biyu a faɗin Najeriya, yayin da aka riga aka ba kusan manoma 200,000 tallafin kuɗi.

Ya kuma bayyana cewa an riga an raba buhunan taki sama da miliyan 1.1 a sassa daban-daban na ƙasar nan daga cikin burin raba buhu sama da miliyan 10, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Rahoton WFP: ADC ta zargi Tinubu da jefa miliyoyin mutane cikin yunwa a jihohin Arewa 9

Ya ƙara da cewa an kuma samar da tan 16,470 na ingantattun iri, inda ya ce kamfanonin haɗa manoma guda 20 ne ke kula da aiwatar da shirin a jihohi sama da 20 tare da haɗin gwiwar masu samar da kayan noma 15.

Sotinrin ya ce shirin bai tsaya kan rabon kayan noma kawai ba, domin yana kuma samar da kuɗin tallafi, horon aikin gona da tabbacin sayen amfanin gona bayan girbi.

Ya ce ana ba da kuɗin tallafi lokacin shuka, ana ba da horo yayin noma, sannan bayan girbi ana tattara amfanin gona tare da sayensa cikin farashi mai kyau.

Matar Tinubu ta girbe kayan noma

Mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun nuna cewa uwargidan shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu ta sake girbe kayan lambu daga gonarta da ke Aso Rock Villa a Abuja.

Sanata Remi Tinubu ta buƙaci 'yan Najeriya su rungumi noma a cikin gida domin bunkasa samar da abinci da habaka tattalin arzikin al'umma.

Matar shugaban kasar ta bayyana cewa yin noma a cikin gida na rage kuɗin da maza ke kashewa tare da samar da lafiyayyen abinci ga iyalansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.