Kwanaki bayan ganawa da Tinubu, shahararren gwamnan APC ya magantu akan kudirin takarar shugaban kasa

Kwanaki bayan ganawa da Tinubu, shahararren gwamnan APC ya magantu akan kudirin takarar shugaban kasa

  • Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce a halin yanzu ba ya da burin maye gurbin Shugaba Buhari a 2023
  • Gwamna Akeredolu ya kuma nisanta kansa daga ayyukan kamfen da ke alakanta shi da zaben shugaban kasa na 2023
  • Da yake magana ta hannun hadiminsa, gwamnan ya lura cewa a kwanan ne aka sake zabensa kuma yana son a bar shi ya maida hankali kan jihar Ondo

Akure, jihar Ondo - Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya nisanta kansa daga ayyukan da ke alakanta shi da zaben shugaban kasa na 2023.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa gwamnan na Ondo ya bayyana ci gaban a matsayin wani yunkuri na jan hankali mara amfani.

Kwanaki bayan ganawa da Tinubu, shahararren gwamnan APC ya magantu akan kudirin takarar shugaban kasa
wamna Rotimi Akeredolu ya nisanta kansa daga neman kujerar shugaban kasa Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa matsayin Akeredolu yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Richard Olatunde ya fitar.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Akeredolu ya rattaba hannu kan dokar hana kiwo a fili

Olatunde ya sake nanata cewa ubangidansa ba shi da wata alaƙa da masu kamfen din, jaridar Punch ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa hotunan kamfen na neman Akeredolu ya jefa hularsa cikin raga don tsayawa takarar shugaban kasa na 2023 yana ta yawo a wasu sassan kafofin sada zumunta amma ya nisanta gwamnan daga hakan.

Olatunde ya ce duk da cewa Gwamna Akeredolu yana da 'yancin tsarin mulki, abun da ake bukata da kuma cancantar yin takara, kamfen din na yanzu baya wakiltar shi.

Sanarwar ta ce:

“Saboda haka, Gwamna Akeredolu wanda bai dade ba da aka sake zabarsa yana fatan a bar shi ya mai da hankali kan zurfafa kyakkyawan shugabanci a jihar Ondo.
"Don haka, yana ba da shawara ga duk waɗanda abin ya shafa da su nutsu kamar yadda yake da tabbataccen ra'ayi na cewa Allah ne kaɗai zai iya sanya mutum a wani matsayi."

Kara karanta wannan

Raba-gari: A karshe Shugaba Buhari ya bayyana wadanda ke daukar nauyin IPOB

Legit.ng ta lura cewa sanarwar da ke nisanta Akeredolu daga yakin neman zaben shugaban kasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan gwamnan na jihar Ondo da takwaransa na jihar Ekiti sun ziyarci shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a London.

Duk da cewa bai fito fili ya bayyana sha’awarsa ba, akwai rade-radin cewa Tinubu, tsohon gwamnan Legas, yana son zama shugaban Najeriya bayan ficewar Shugaba Buhari.

2023: A karshe Tinubu ya samu daidai da shi yayin da jiga-jigan PDP suka marawa tsohon gwamna baya

A wani labari na daban, mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Bamaina da ke karamar hukumar Birnin Kudu ta Jigawa sun bukaci tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

‘Ya’yan babbar jam’iyyar adawar kasar sun bayyana haka ne a wani karamin taro da aka yi a garin Lamido a ranar Talata, 31 ga watan Agusta, jaridar PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An sassauta doka: Mazauna Jos sun garzaya kasuwanni domin sayen kayan abinci

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Dr. Ibrahim Babandi ya dage cewa lallai sai Lamido ya shiga takarar shugaban kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng