An kuma: PDP ta sake lallasa APC a jihar Kaduna a zaben kananan hukumomi a Jaba
- A ci gaba da sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi a Kaduna, PDP ta sake lashe zabe
- An gudanar da zaben na kananan hukumomi ne a ranar Asabar da ta gabata, kuma an fara sanar da sakamako
- A karamar hukumar Jaba, wani dan takarar jam'iyyar PDP ya lashe zabe, inda ya lallasa dan takarar APC
Kaduna - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna ta ayyana Mista Phillip Gwada dan jam'iyyar PDP, a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugabancin karamar hukumar Jaba da aka yi ranar Asabar 4 ga watan Satumba.
Baturen zabe, Farfesa Peter Omale, ya bayyana hakan a ranar Litinin 6 ga watan Satumba a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar, SIEC, a Kwoi, inji rahoton Daily Nigerian.
Mista Omale ya ce Gwada ya samu kuri'u 9,012 inda ya lallasa dan takarar APC, Mista Benjamin Jock, wanda ya samu kuri'u 5,640.
Ya ce dan takarar jam'iyyar ADP, Alhamdu Gyet, ya zo na uku da kuri'u 2,732.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Mista Omale:
“Mista Phillip Gwada na PDP, bayan ya cika ka’idojin doka kuma ya sami mafi yawan kuri’un an tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zabe kuma shi aka zaba.”
Jam'iyyar PDP Ta Lallasa El-Rufa'i da APC a Zaɓen Kansila Na Gundumar Gwamnan Kaduna
Dan takarar jam'iyyar PDP ya lashe zaɓen kansila da aka gudanar a Unguwan Sarki, gundumar gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen, baturen zaɓen gundumar, Mohammed Usman, yace ɗan takarar PDP, Abdulhalim Na’ibi, ya samu kuri'u 1,405.
Yayin da ya kada abokin takararsa na jam'iyyar APC mai mulki, Aliyu Farouk, wanda ya samu kuri'u 804.
Rikicin Jos: El-Rufa'i ya yi alkawarin magance matsalar tsaro a Jos da Kaduna
A wani labarin, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da takwaransa na jihar Filato, Simon Bako Lalong, sun yi alkawarin hada kai da rundunar Operation Safe Haven (OPSH) da sauran hukumomin tsaro don magance matsalolin tsaro da ke addabar jihohin biyu.
Sun yi wannan alkawari ne ranar Lahadi 5 ga watan Satumba lokacin da El-Rufai ya ziyarci Lalong don jajantawa gwamnati da mutanen jihar Filato kan hare-hare da kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamna El-Rufai ya ce:
“Filato da Kaduna ba makwabta ne kawai ba. Muna da dangantaka mai karfi kuma tun lokacin da muka hau mulki a 2015, ni da Gwamna Lalong muna tuntubar juna; Gwamna Lalong ne ya gabatar da mu ga Cibiyar Tattaunawar Ba da Agaji, wata kungiya mai zaman kanta ta duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya."
Asali: Legit.ng