Siyasar Najeriya
Shugaban jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) na kasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce APC za ta fadi a zaben 2027 idan an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya buƙaci Bola Tinubu ya kare dimokuraɗiyya, ya bai wa adawa damar yin aiki cikin ’yanci, tare da shawartar ’yan Najeriya.
Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce APC za ta lashe zaben gwamnan Osun ta hanyar tsarin siyasa ba karfin tarayya ba.
Ministan Ayyuka Dave Umahi ya ce Tinubu yana da kyakkyawar niyya ga Kudu maso Gabas, yana mai cewa gwamnati na aiwatar da muhimman ayyukan raya yankin.
Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa an shirya makircin kama tsohon gwamna kuma sakataren jam'iyyar na ƙasa, Rauf Aregbesola, dab da zaɓen gwamna ranar Asabar.
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce rashin sake zaɓen Tinubu a 2027 zai zama kuskure, yana jaddada ci gaban gwamnatin jam'iyyar APC.
ADC ta tsayar da Mamman Musa a matsayin abokin takarar Mohammed Kpautagi a jihar Neja, inda jam’iyyar ta kafa tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen 2027.
Dan takarar gwamnan Kaduna na ADC, Isa Ashiru, ya nada John Markus Ayuba a matsayin Darakta-Janar na kwamitin kamfen domin shirye-shiryen zaben 2027
Hukumar INEC ta ƙara ɗan takarar jam'iyyar SDP, Francis Ajala, cikin zaɓen gwamnan Osun bayan hukuncin kotu, inda jam’iyyun da za su fafata suka koma 15.
Siyasar Najeriya
Samu kari