Rikicin ADC: Kotu Za Ta Yi Zama kan Shari'ar Nafiu Bala da Tsagin David Mark

Rikicin ADC: Kotu Za Ta Yi Zama kan Shari'ar Nafiu Bala da Tsagin David Mark

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsayar da ranar Juma’a, 8 ga watan Mayu 2026, domin ci gaba da shari’ar rikicin shugabancin jam’iyyar ADC
  • Wannan ya biyo bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a karar da David Mark ya shigar, inda aka umarci babbar kotun ta ci gaba da saurari shari'ar
  • Rikicin ya fara ne bayan Nafiu Bala Gombe ya shigar da ƙara, yana ƙalubalantar David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugabannin ADC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sa ranar Juma'a, 8 ga watan Mayu, domin sauraron shari'ar rikicin shugabancin jam'iyyar ADC tsakanin Nafiu-Bala Gombe da tsagin Sanata David Mark.

A ranar Laraba ne aka tattaro cewa an riga an aika wa ɓangarorin da abin ya shafa takardar gayyata domin su bayyana a gaban mai shari'a, Mai shari'a Emeka Nwite.

Kara karanta wannan

'Ka yi da matata, in yi da matarka,' An kama abokai da ke musayar matansu a Bauchi

Kotu za ta saurari shari'ar rikicin ADC tsakanin Nafiu Bala da tsagin David Mark
Hagu zuwa dama: David Mark, Nafiu Bala Gombe da Atiku Abubakar. Hoto: @atiku, @SenDavidABMark, @Imranmuhdz
Source: Twitter

ADC: Za a saurari shari'ar Nafiu Bala

Mai shari'a Nwite ya tsayar da wannan rana ne biyo bayan wata wasiƙar neman ranar sauraron ƙara mai lamba FHC/ABJ/1819/2025, wadda lauyan mai ƙara, Luka Haruna (SAN), ya shigar, in ji rahoton Daily Trust.

Wasiƙar, wadda aka rubuta aka kuma shigar a ranar 5 ga Mayu, ta bayyana cewa:

“Biyo bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke a ranar 30 ga Afrilun 2026 kan ƙarar da Sanata David Mark ya shigar, muna neman a ba mu rana domin gaggauta sauraron wannan magana daidai da hukuncin kotun daukaka kara.
"A tare da wannan takarda, akwai kwafin hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, wacce ta bukaci a gaggauta sauraro da yanke hukunci a wannan shari'ar."

A ranar 14 ga Afrilu, 2026, Mai shari'a Nwite ya ɗage sauraron shari'ar har sai abin da hali ya yi, biyo bayan buƙatar Nafiu Gombe na jiran hukuncin Kotun Ƙoli kan karar da Mark ya shigar.

Kara karanta wannan

Bayan shigar Kwankwaso da Obi, NDC ta fadi 'yan takarar da za ta tsaida a 2027

Shari'ar rikicin shugabancin jam'iyyar ADC

Nafiu Bala Gombe, wanda tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC ne na ƙasa, ya shigar da ƙarar ne domin neman kotu ta hana David Mark (Shugaban Jam’iyya) da Ogbeni Rauf Aregbesola (Sakataren Jam’iyya) ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar.

Ya shaida wa kotu cewa bayyanar Mark da Aregbesola a matsayin shugabannin jam’iyyar ya saɓa wa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma Dokar Zaɓe ta ƙasa.

Sai dai, David Mark, wanda ake kara na biyu a shari'ar da Nafiu ya shigar a babbar kotun tarayya, ya kai maganar zuwa Kotun Koli don kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara na ranar 12 ga Maris.

Nafiu Bala Gombe ya na neman kotu ta rusa shugabancin David Mark a jam'iyyar ADC.
Nafiu Bala Gombe, wanda ke ikirarin shugabancin jam'iyyar ADC. Hoto: Nafiu Bala
Source: Facebook

Bukatar Nafiu Gombe kan shari'ar ADC

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025, Nafiu Gombe ya shigar da ƙarar jam'iyyar ADC, David Mark, Rauf Aregbesola, Hukumar Zaɓe ta INEC, da kuma Ralph Nwosu.

Babban burin Nafiu Bala Gombe shi ne kotu ta tabbatar da cewa, an bi haramtacciyar hanya wajen nada shugabancin su David Mark, sannan kotu ta hana wadanda ake kara gudanar da taro ko jagorantar ayyuka da sunan ADC.

Kara karanta wannan

An yaye daga ADC, 'yan majalisa 17 sun bi Kwankwaso da Obi zuwa NDC

Ana yi wa Nafiu Bala barazana?

A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban tsagin ADC a Najeriya, Nafi’u Bala ya yi magana game da barazanar da aka ce an yi masa kan jam'iyyar adawa.

Bala, wanda ya tsaya takarar gwamna a Gombe ƙarƙashin ADC a zaɓen 2023, ya ce rahoton da ke ikirarin rayuwarsa na cikin haɗari ƙarya ne.

Rahoton ya ambato Bala yana cewa bai yi tsammanin rikicin siyasar cikin jam’iyyar zai kai wannan matsayi mai muni da ya gagari shawo kansa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com