ADC Ta Fadi Yadda Fitar Obi da Kwankwaso zai Zamo Mata Gobarar Titi
- Shugaban jam'iyyar ADC na kasa, David Mark ya yi martani kan sauya shekar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi suka yi
- David Mark ya bayyana cewa duk da sauya shekar Kwankwaso da Obi abu ne da ba za a so ba, hakan zai karawa 'yan ADC himma
- Sanata Kwankwaso da Peter Obi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta NDC yayin da rikicin cikin gida ke kara tsananta a jam'iyyar ADC
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam'iyyar adawa ta ADC ta yi martani kan sauya shekar da tsofaffin 'yan takarar shugaban kasa biyu suka yi daga tafiyarta.
'Yan takarar shugaban kasa a NNPP da LP, Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun sauya sheka daga jam'iyyar ADC zuwa NDC.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban jam'iyyar ADC na kasa, Sanata David Mark ne ya yi magana kan sauya shekar shugabannin.
Maganar shugaban ADC na kasa
Shugaban jam’iyyar ADC na kasa, Sanata David Mark, ya amince cewa ficewar tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar zai yi tasiri, amma ya ce hakan zai sa su kara kaimi wajen aiki.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa jam’iyyar za ta tsayar da sahihan ‘yan takara masu karfin lashe zabe a shekarar 2027.
Da yake jawabi ranar Laraba a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja yayin da yake ganawa da mambobin kungiyar ‘yan majalisar tarayya na ADC, Mark ya ce jam'iyyar za ta yi nasara.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa kalubalen da jam’iyyar ke fuskanta zai kara mata karfi tare da taimaka mata ta samu nasara a zabe.
Magana kan Kwankwaso da Obi
Da yake magana kan ficewar Obi da kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, Leadership ta wallafa cewa David Mark ya ce:

Kara karanta wannan
Ganduje ya kara tsokano Kwankwaso, ya kwatanta shi da 'tsuntsu' a siyasar Najeriya
“Babu shakka, ficewar Obi da Kwankwaso na da tasiri, amma hakan zai sa mu kara himma wajen aiki.”

Source: Facebook
Tun da farko, sakataren yada labarai na kasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar ba ta damu da sauya shekar ‘yan majalisa ba, yana cewa manyan tsare-tsaren jam’iyyar na nan daram.
Bolaji Abdullahi ya zargi ‘yan majalisar da suka fice da bin wasu mutane ne kawai da suke ganin za su taimaka musu wajen samun nasara a zabe.
Ya ce:
“Mutanen da suka fice sun bi wadanda da suke ganin za su taimaka musu su ci zabe. Muna masu fatan alheri, amma manyan tsare-tsaren jam’iyyarmu na nan daram.”
Ana so Atiku ya koma NDC
A wani labarin, kun ji cewa na hannun daman Sanata Rabiu Kwankwaso, Buba Galadima ya yi kira ga Atiku Abubakar da ya koma NDC.
Buba Galadima ya bayyana cewa lokaci ya yi da duk mai son ceto Najeriya zai shiga jam'iyyar NDC domin adawa da gwamnatin Bola Tinubu.
Ya yi kira ga Atiku Abubakar ne kwanaki kadan bayan Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun sauya sheka sun bar Atiku a ADC.
Asali: Legit.ng
