‘Yadda Tinubu Ya Tilastawa Kwankwaso da Peter Obi Haduwa a Jam’iyya 1’
- Jigon ADC a Najeriya, Dele Momodu ya yi magana game da siyasar zaben shekarar 2027 da ake tunkara a fadin kasar
- Momodu ya ce matsin lambar siyasar Shugaba Bola Tinubu ne ya tilasta Peter Obi da Rabiu Kwankwaso hada kai
- Dan siyasar ya bayyana cewa sauyin jam’iyya da hadakar ‘yan adawa ba tabbacin nasara ba ne, yana mai cewa yanayin siyasar Najeriya ya sauya sosai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fitaccen dan siyasa kuma mawallafin mujallar Ovation International, Dele Momodu, ya magantu kan siyasar zaben 2027.
Momodu ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya haddasa haduwar wasu manyan ‘yan adawa kafin zaben shugaban kasa na 2027.

Source: Facebook
Momodu, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.
'Abin da ya hada kan Kwankwaso da Obi'
Ya ce matsin lambar siyasa daga gwamnatin APC ne ya sa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suka fara aiki tare domin neman mafita a siyasar kasar nan.
Ya ce:
“Tinubu ne ya tilasta masu gaba daya su hade kai. Shi ya sa suka fara tafiya a hanya daya, wanda da zai zama abin kyau idan ya rikide zuwa fafatawar jam’iyyu biyu."
Tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, da Rabiu Kwankwaso na NNPP sun fice daga ADC zuwa NDC bayan matsalolin shari’a da suka dabaibaye kawancen jam’iyyar.
Sauyin nasu ya jawo ce-ce-ku-ce kan yiwuwar kafa tikitin hadin gwiwa tsakanin Obi da Kwankwaso domin kalubalantar Tinubu a 2027.
Sai dai Momodu ya yi gargadin cewa siyasar Najeriya ta canza sosai tun bayan zaben 2023, yana mai cewa babu tabbacin cewa ‘yan takarar za su iya rike dukkan kuri’un da suka samu a baya.

Kara karanta wannan
Ganduje ya kara tsokano Kwankwaso, ya kwatanta shi da 'tsuntsu' a siyasar Najeriya
“Wa ya tabbatar Tinubu zai sake samun kuri’u sama da miliyan takwas da ya samu a baya? Kuma wa ya tabbatar Obi da Kwankwaso za su iya rike duk masu zaben su?”
- Dele Momodu

Source: Facebook
Jigon ADC ya ce kofarsu a bude take
Momodu ya kuma yi nuni da yadda wasu gwamnoni na kungiyar G5 suka kasa samun kujerun Sanata a jihohinsu a matsayin hujjar cewa ra’ayin masu kada kuri’a yana sauyawa.
Da yake magana kan hadakar ‘yan adawa, ya ce ADC za ta ci gaba da bude kofarta ga masu son shiga, amma ba za ta amince da matsin lamba daga kowa ba.
Momodu ya tunatar da cewa hadakar Atiku Abubakar da Peter Obi a 2019 ba ta kawo nasara ba, haka kuma rabuwar da suka yi a 2023 ma ba ta kayar da jam’iyya mai mulki ba.
A karshe, ya bukaci ‘yan siyasa su kwantar da hankalinsu tare da yin siyasa cikin hikima maimakon firgita da yanayin siyasar da ake ciki.
Rigima ta kunno kai a jam'iyyar ADC
An ji cewa shirin tsayar da dan takara daya a zaben 2027 na jam'iyyun adawa, rikici ya kara tsananta a tsakaninsu saboda wasu sauye-sauye.
Hakan na da nasaba da ficewar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso daga hadakar ADC zuwa jam'iyyar NDC gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Magoya bayan Atiku Abubakar sun ce shirin tsayar da dan takara daya tilo domin kalubalantar Bola Tinubu a 2027 yana nan daram.
Asali: Legit.ng

