Matasa Sun Yi Cincirindo a Gidan Jonathan kan Zaben Shekarar 2027, Sun Fadi Bukatarsu
- Tsohon shugaban kasa, Dr Goodluck Ebele Jonathan, ya ga dandazon wasu matasa da suka je gidansa a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2026
- Matasan wadanda suka yi cincirindo a gidan tsohon shugaban kasar da ke Maitama a Abuja, sun rika wakoki da raye-raye na nuna goyon baya a gare shi
- Sun bukaci Jonathan da ya fito a dama da shi domin shiga takarar shugaban kasa a zaben 2027, inda suka bayyana shi a matsayin wanda zai iya ceto Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wata ƙungiyar matasa, a ƙarƙashin inuwar haɗakar masu goyon bayan Goodluck Jonathan, sun yi zanga-zanga a gidansa.
Matasan sun taru a gidan tsohon shugaban ƙasa da ke Abuja domin nuna gagarumin goyon baya kan ya fito takara a zaben 2027.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa matasan sun taru a gidan tsohon shugaban kasar ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayun 2026.
Matasa na son Jonathan ya fito takara a 2027
Sun rera waƙoƙi tare da rera taken kira ga Jonathan da ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Masu zanga-zangar sun mamaye yankin Taraba Close da ke Maitama, inda suka cika titunan da ke kusa, lamarin da ya haddasa gagarumin cikas ga zirga-zirgar ababan hawa a unguwar ta masu hannu da shuni.
Sun rerawa Jonathan wakoki
Sun gudanar da raye-raye tare da ɗaga allunan sanarwa masu ɗauke da saƙonni kamar su: ‘GEJ: Najeriya na mutuwa, cece ta!’, ‘GEJ, matasan Najeriya sun karya asirin da aka yi maka’, da kuma ‘GEJ, idan ba ka tsaya takara ba, mun mutu’.
Matasan sun bayyana Jonathan a matsayin jagora mai haɗa kan al’umma wanda yake da ikon ceton ƙasar daga ƙalubalen da take fuskanta a halin yanzu.
Wannan taro na nuna goyon baya ya ƙara yawan kiran da ƙungiyoyi daban-daban ke yi na neman tsohon shugaban ƙasar ya dawo fagen siyasa gabanin zaɓen 2027.
Jonathan ya yi jawabi
Jonathan ya bayyana cewa ya ji kiran da suke yi, amma zai gudanar da tuntuɓa mai faɗi kafin ya ɗauki kowace irin shawarar siyasa, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga matasan Najeriya da su zurfafa shiga cikin ayyukan dimokuraɗiyya, musamman wajen tabbatar da gudanar da zaɓubbuka cikin lumana, inganci, da kuma gaskiya a faɗin ƙasar.

Source: Facebook
Ya nuna damuwarsa kan raguwar yawan masu fita zaɓe, inda ya bayyana karancin masu fita kada kuri'ar zaɓe a matsayin babban ƙalubale da ke fuskantar dimokuraɗiyyar Najeriya.
"Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi kowane matakin rashin fita zaɓe a cikin dukkan zaɓubbukan da na sanya ido a kansu a duniya."
- Goodluck Jonathan
Jonathan ya yi wa Atiku martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi martani kan wasu kalamai da Atiku Abubakar, ya yi a kansa.

Kara karanta wannan
Bayan abin da ya faru, an haramta wa masu digirin girmamawa amfani da 'Dr' a Najeriya
Goodluck Jonathan ya kare gwamnatinsa, inda ya ƙara da cewa ya yi iya kokarinsa lokacin da yake kan mulki.
Tsohon Shugaban ya kare shawarwarin da ya ɗauka a ofis, yana mai cewa yayin da kuskure yake tabbatacce, shi dai ya yi iya ƙoƙarinsa.
Asali: Legit.ng

