"Babu Irina": Peter Obi Ya Bayyana Bambancinsa da Kwankwaso
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, Peter Obi, ya bayyana bambancinsa da sauran masu neman shugabancin Najeriya
- Peter Obi ya bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fi shi samun matsayi a fannin ilmi inda yake da PhD
- Hakazalika, Peter Obi, ya bayyana cewa Najeriya tana bukatar shugaba irinsa wanda ya kware wajen samar da arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya bayyana abin da Najeriya ta ke bukata.
Peter Obi ya bayyana cewa abin da Najeriya ke buƙata a yau shi ne mutumin da zai iya samar da arziki kuma ya gudanar da shi yadda ya dace.

Source: Facebook
Obi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da shugaban tashar News Central, Kayode Akintemi, a cikin shirin ‘60 Minutes with Kay’ wanda aka sanya a Youtube a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026.
Peter Obi ya ce babu wani mai neman takarar shugaban ƙasa, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, da zai iya gogayya da ƙwarewarsa a fannin samar da arziki.
Me Kwankwaso ya ce kan Obi a baya?
Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga Sanata Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, wanda ya bayyana a cibiyar Chatham House da ke London a shekarar 2023 cewa yana da digirin digirgir (PhD) kuma ya fi cancantar zama shugaban ƙasa maimakon zama mataimakin Obi.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a wancan lokacin.
A yanzu haka dai mutanen biyu sun koma jam’iyyar NDC, inda ake kyautata zaton Kwankwaso zai zama mataimakin Obi a zaɓen 2027 bayan da jam’iyyar ta ware takarar shugaban ƙasa ga yankin Kudu, inda Obi ya fito.
Wane martani Peter Obi ya yi?
“Cancanta ra’ayi ne kuma ya dogara da inda ka fito. Shi (Kwankwaso) ya ce ya fi cancanta saboda yana da PhD, wanda hakan ba shi da aibu. Ni ba ni da PhD."
“Kwankwaso ya zuba jari a wani muhimmin fanni na ci gaba, wato ilimi. Ci gaba ba a auna shi da dogayen gine-gine ko gadojin sama ba.”
“Yana da ɗan ƙwarewa, kuma ya waye. Ya taɓa yin Minista. Babu shakka game da hakan. Ba na jin ikirarinsa ba daidai ba ne, amma ga abin da Najeriya ke buƙata a yau, Najeriya tana buƙatar mai samar da arziki da kuma mai gudanar da arziki.”
“Na gina manyan kasuwanci sanannu masu kyakkyawan suna tun daga tushe a gida da kuma ƙasashen waje. Babu wani a yau a cikin wannan fagen, har da shugaban ƙasa, da zai iya ikirarin yana da irin ƙwarewa ta.”
“Abin da Najeriya ke buƙata a yau shi ne wanda ke samar da arziki, ba wanda ke raba arziki ba; mutumin da zai iya gudanar da albarkatu cikin mafi inganci da kuma tanadi domin gobe."
- Peter Obi

Source: Facebook
Jigo a ADC ya soki Kwankwaso, Obi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi sun sha ragargaza daga wajen jigo a jam'iyyar ADC, Kenneth Okonkwo.
Kenneth Okonkwo ya soko tsofafffin gwamnonin ne kan shawararsu ta barin haɗakar jam’iyyar ADC zuwa jam’iyyar NDC.
Okonkwo ya yi zargin cewa Obi da Kwankwaso sun bar ADC ne saboda ba su shirya gudanar da zaɓen fitar da gwani a cikin jam’iyyar ba.
Asali: Legit.ng

