"Rashin Tsaro na Barazana ga Sahihin Zabe"; Shugaban INEC Ya Kawo Mafita kan 2027

"Rashin Tsaro na Barazana ga Sahihin Zabe"; Shugaban INEC Ya Kawo Mafita kan 2027

  • Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Farfesa Joash Amupitan, ya nuna damuwa kan bukatar gudanar da sahihin zabe
  • Farfesa Amupitan ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro na barazana ga gudanar da sahihin zabe a Najeriya
  • Shugaban na INEC ya nuna muhimmancin da ke akwai wajen yin hadin gwiwa da hukumomin tsaro domin magance matsalar

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi magana kan zaben shekarar 2027.

Farfesa Amupitan ya yi gargaɗin cewa yanayin rashin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya yana barazana ga gudanar da zaɓubbuka cikin adalci da gaskiya.

Shugaban INEC ya ce akwai barazana kan zabe a Najeriya
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa Amupitan ya yi wannan jawabin ne yayin ziyarar da ya kai wa shugaban ƴan sandan Najeriya, Tunji Disu, ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026 a Abuja.

Kara karanta wannan

NDC ta buɗewa Obi ƙofa, ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa ga Kudancin Najeriya

Wane kalubale ake fuskanta kan zabe?

Farfesa Amupitan ya ce ƙalubalen tsaro da ake fuskanta, waɗanda suka haɗa da tashe-tashen hankula da barazana ga tsarin zaɓe, za su iya raunana ingancin zaɓe idan ba a shawo kansu yadda ya kamata ba.

"A Najeriya, tsarin zaɓenmu ya fuskanci ƙalubale da dama tsawon shekaru, kama daga maguɗi zuwa barazanar tashin hankali, da sayen ƙuri’u waɗanda ke rage kwarin gwiwar masu zaɓe."
“Waɗannan ƙalubalen ba wai kawai suna shafar sakamakon zaɓukanmu ba ne, har ma suna haifar da babban haɗari ga tsaron ƙasarmu. Don haka, yana da muhimmanci mu fuskanci waɗannan matsalolin da cikakken muhimmanci da azama. A kan wannan, ina so na jaddada mahimmancin ɗaukar matakan tsaro tun da wuri."
“Yanayin rashin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya na zama barazana ga gudanar da zaɓe cikin adalci. Yana da muhimmanci mu gudanar da cikakken binciken haɗarin tsaro gabanin zaɓen."
"Hakan zai ba mu damar gano wuraren da ake fuskantar barazana da kuma tsara dabarun da suka dace don rage haɗari, ta yadda za a kare masu zaɓe, jami’an zaɓe, da kuma mutuncin tsarin zaɓen.”

Kara karanta wannan

APC ko ADC: Gwamna Makindee ya fadi jam'iyyar da za ta samar da shugaban kasa a 2027

- Farfesa Joash Amupitan

Shugaban INEC ya yi magana kan zaben 2027
Farfesa Joash Amupitan a jawabi a wajen taro Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Wadanne matakai INEC ke so a dauka?

A cewarsa, irin waɗannan matakan za su taimaka wajen gano wuraren da rikici zai iya tashi da kuma ba da damar tura dabarun kare masu zaɓe da jami’an zaɓe, jaridar Daily Trust ta kawo rahoton.

Farfesa Amupitan ya bayyana cewa zaɓubbukan da aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga Janairu, 2027 (na shugaban ƙasa) da 6 ga Fabrairu, 2027 (na gwamnoni da majalisun jiha) suna buƙatar haɗin kai mai ƙarfi tsakanin INEC da hukumomin tsaro, musamman ƴan sandan Najeriya, waɗanda su ne ke jagorantar ayyukan tsaron zabe.

INEC za ta gudanar da zaben cike gurbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta shirya gudanar da zabubbukan cike gurbi.

Rahotanni sun nuna cewa INEC ta ce za a gudanar da zaɓukan cike gurbin tare da zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da aka tsara a rana guda.

A INEC, zaɓubbukan za su haɗa da kujerun sanatoci a jihohin Enugu, Nasarawa, Rivers da Ondo, da kuma kujera ta Majalisar Dokokin Jihar Kebbi da kujera ta Majalisar wakilai a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng