Wike vs Turaki: 'An Ruguza Yunkurin Hana PDP Tsaida Dan Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027'

Wike vs Turaki: 'An Ruguza Yunkurin Hana PDP Tsaida Dan Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027'

  • Tsagin Tanimu Turaki ya ce yunkurin da Ministan Abuja, Nyesom Wike da masu mara masa baya suka yi na hana PDP tsaida dan takara bai ci nasara ba
  • Wannan kalamai na zuwa ne bayan Wike ya soki bangaren Tanimu Turaki SAN, inda ya zarge su da saba wa hukuncin da Kotun koli ta yanke
  • Mai magana da yawun kwamitin rikon kwarya na PDP, Ini Ememobong ya ce ya fahimci abin da ya fusata ministan kuma ba yadda zai yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam'iyyar PDP ta tsagin Tanimu Turaki ta yi ikirarin cewa duk wani yunkuri da wasu tsiraru suka yi na hana jam'iyyar tsaida dan takarar shugaban kasa a zaben 2027 bai cimma nasara ba.

Kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki ne ya bayyana hakan bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke a makon jiya.

Kara karanta wannan

"Ba a fahimce ni ba," Ganduje ya bayyana dalilin kiran Sanusi II a matsayin Sarkin Kano

Shugaban PDP.
Shugaban tsagin jam'iyyar PDP na kasa, Tanimu Turaki (SAN) a ofis Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Tsagin Tanimu Turaki ya rusa shirin Nyesom Wike

Ya bayyana cewa shirin da wasu jagororin bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike suka yi na hana jam’iyyar fitar da dan takarar shugaban kasa ya ci tura, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwamitin na wucin gadi ya yi wannan furuci ne domin mayar da martani ne ga kalaman Ministan Babban Birnin Tarayya (Abuja), Nyesom Wike, ya yi.

Mista Wike, a wata tattaunawa da manema labarai ranar Laraba ya zargi kwamitin Turaki da saba wa hukuncin kotu tare da kalubalantar shugabannin bangaren Turaki su bude asusun banki da sunan jam’iyyar.

Martanin tsagin PDP ga Ministan Abuja

Sakataren yada labarai na kwamitin rikon kwaryar, Ini Ememobong, ya ce ministan ya shiga yanayin bakin ciki ne saboda sun riga sun fara tafiyar da asusun jam’iyyar PDP.

Ya ce sun fahimci Wike na cikin bakin ciki saboda ya ga jam'iyyar na shirye-shiryen tsaida dan takarar shugaban kasa, sabanin yadda ya tsara na hana tsaida wanda zai kara da Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

"Haka Allah ya tsara," 'Dan takarar APC, Jamilu Gwamna ya nemi hadin kan Pantami a Gombe

Ememobong ya ce:

“Mun fahimci takaicinsa dangane da fara sayar da fom da kuma shirye-shiryen gudanar da zabukan fitar da gwani da kuma babban taro na kasa inda za a fitar da sahihin dan takarar shugaban kasa.”
Wike.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike yana magana da manema labarai Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Facebook

Tsagin Turaki sun fara sayar da fam

Ya kara da cewa ana ci gaba da sayar da fam din kuma babu abin da Wike zai iya yi domin dakatar da hakan, kamar yadda Punch ta rahoto.

“Barazanar da yake yi cewa zai dauki mataki kan bankunan da za su bude mana asusu ba gaskiya ba ce, domin ya san cewa muna gudanar da asusun jam’iyyar, shi ya sa tawagar abokansa ke karbar kudi ta asusun mutane daban-daban,” in ji shi.

PDP ta ba dan Sule Lamido takara

A wani labarin, kun ji cewa Mustapha Sule Lamido, wanda ya yi takarar gwamnan Jigawa a zaben 2023 karkashin PDP, ya sake nuna sha'awar neman takara a 2027.

Kara karanta wannan

"Idan kun isa": Wike ya kalubalanci bangaren Turaki kan rikicin PDP

Tsohon dan takarar ya karbi fom din tsayawa takara kuma ya mika shi ga kwmaitin gudanarwa na jam'iyyar PDP da sauran masu ruwa da tsaki.

Bayan haka, PDP ta amince ta sake bai wa 'dan Sule Lamido takarar gwamnan Jigawa karo ma biyu, inda aka ji Mustapa ya fito yana mika godiya ga jam'iyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262