"Idan Kun Isa": Wike Ya Kalubalanci Bangaren Turaki kan Rikicin PDP
- Jam'iyyar PDP na ci gaba da fuskantar rikicin gida tsakanin bangarorin Nyesom Wike ke goyawa baya da na Tanimu Turaki
- Ministan na Abuja ya fito ya kalubalanci bangaren Tanimu Turaki kan bude ofishi da kuma asusun bankin da za su yi amfani da shi
- Nyesom Wike ya bayyana cewa ba zai zauna ya zura ido yana gani bangaren Turaki na yi wa doka hawan kawara ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ƙalubalanci ɓangaren Tanimu Turaki na jam’iyyar PDP.
Wike ya ƙalubalance su da su buɗe sakatariyar jam’iyyar a hukumance a Abuja da kuma asusun banki idan har da gaske sun yarda cewa su ne ke iko da jam’iyyar adawar.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa Wike ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja a ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026.
Ministan ya yi alƙawarin rurrufe duk wani ofishi da za a kafa a Abuja muddin aka buɗe shi da sunan bangaren Turaki.
Wike ya ragargaji bangaren Turaki na PDP
Wike ya soki ɓangaren da Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da Turaki da sauran su ke jagoranta, inda ya zarge su da zamba, yin kunnen uwar shegu da hukuncin kotu da gangan, da kuma wani shiri na yaudarar ’yan Najeriya.
“Yaushe ne mutane za su daina damfara? Ba za ka iya saɓawa hukuncin kotu ba sannan ka dawo kana yaudarar ’yan Najeriya cewa kana da sahihin tsari. Hakan ba shi ne yadda dimokuradiyya ke aiki ba."
- Nyesom Wike
Wike ya ce shari'a ba ta san da su ba
Ministan, wanda tsohon gwamnan jihar Rivers ne, ya nace cewa ɓangaren da ke adawa da shugabancin jam’iyyar da aka sani ba shi da wani matsayi na shari’a da zai gudanar da harkokin PDP, jaridar TheCable ta kawo rahoton.
“Ba za ku ci gaba da yaudarar ’yan Najeriya ba. Idan suna da tabbacin cewa su ne halastaccen shugabancin PDP, to su buɗe asusun PDP na hukumance su gaya wa mambobin jam’iyyar su biya kuɗin fom ɗin takara a ciki."

Kara karanta wannan
APC ko ADC: Gwamna Makindee ya fadi jam'iyyar da za ta samar da shugaban kasa a 2027
- Nyesom Wike
Wike ya bayyana cewa babu wata cibiyar kuɗi da za ta karɓi irin wannan buƙata saboda ɓangaren ba shi da takardun jam’iyyar na asali da kuma tsarin shugabancin da doka ta amince da shi wanda bankuna ke buƙata kafin mu’amala.

Source: Facebook
Wike ya yi wa bangaren Turaki barazana
Dangane da batun ofishi kuwa, Wike ya fito fili ya yi barazanar yin amfani da ikonsa na Ministan Abuja idan suka kuskura suka bude shi.
“Ba ka kafa shugabanci a cikin ɗakin kwananka ka kira shi tsarin ƙasa ba. Bari su buɗe ofishi a ko’ina su kira shi sakatariyar PDP, na ƙalubalance su. Ta hakan ne za ka san gaskiya da kuma ƙarya."
“Idan wani ya kuskura ya buɗe haramtaccen ofishi da sunan PDP a Abuja, zan rurrufe shi. Ba zan bar wani ya tayar da hankali ba saboda aikina shi ne tabbatar da doka da oda a babban birnin tarayya."
- Nyesom Wike
Tsohon ministan Tinubu zai yi takara a PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a boye.
Uche Nnaji ya fice daga APC ne bayan ya sauka daga mukaminsa na minista a watan Oktoba na shekarar 2025.
Duk da cewa yana ƙarƙashin binciken hkumar ICPC, Nnaji na ci gaba da yunƙurin tsayawa takarar gwamnan jihar Enugu a 2027.
Asali: Legit.ng

