Za a Fara da Gaske: Atiku, Amaechi Sun Mayar da Fom din Neman Takarar 2027

Za a Fara da Gaske: Atiku, Amaechi Sun Mayar da Fom din Neman Takarar 2027

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, sun miƙa fom ɗin neman tsayawa takarar shugaban ƙasa
  • Manyan masu neman takarar shugaban ƙasa biyu a ƙarƙashin ADC sun miƙa fom ɗinsu a hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis
  • A cikin wani bayani da ya yi bayan mika fom din, Atiku ya bayyana wannan mataki a matsayin babban ci gaba wajen dawo da martabar Najeriya bayan 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi sun miƙa fom ɗin neman takararsu a hedikwatar jam’iyyar ADC da ke Abuja a ranar Alhamis.

Amaechi ya yi alƙawarin gyara Najeriya cikin shekara huɗu idan aka zaɓe shi, yana mai cewa ƙwarewa da gogewa da ayyukan da mutum ya yi ne ya kamata su ba shi damar takara a 2027, ba ƙabila ko son zuciya ba.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin gwamna ya samu tikitin takara, zai kara da Gwamnan Sokoto

Rotimi Amaechi da Atiku Abubakar
Lokacin da Rotimi Amaechi da Atiku Abubakar suka mayar da fom din takara. Hoto: Rt Hon Chibuike R Amaechi|Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku Abubakar ya mika fom din takara

Atiku, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, ya ce takararsa ta shugaban ƙasa tana wakiltar wani gagarumin yunƙuri na dawo da ci gaba da sake gina Najeriya.

Da yake magana bayan miƙa fom ɗinsa a hedikwatar ADC ta ƙasa da ke Abuja, Atiku ya rubuta cewa:

“Yunƙurin dawo da martaba da cigaba ga ƙasarmu mai daraja ya ɗauki mataki mai ƙarfi kuma mai muhimmanci a yau a hedikwatar jam’iyyarmu ta ADC.”

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce batun takarar shi ta wuce batun siyasa kawai, ya ce tana da alaƙa da sabunta Najeriya da dawo da cigabanta a duniya.

“Wannan yunƙuri ne na ƙasa da aka gina kan fatan kawo cigaba da kuma ƙudurin haɗin kai domin ceto Najeriya daga halin da take ciki,”

In ji Atiku Abubakar.

Ameachi ya maida fom din takarar ADC

Kara karanta wannan

Amaechi ya mika fom din neman takara a ADC, ya fadi a lokacin da zai gyara Najeriya

Amaechi ya yi alƙawarin kawo sauyi a shekara hudu jim kaɗan bayan miƙa fom ɗinsa, inda ya kuma soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana ɗaura mata alhakin taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasar.

Tsohon gwamnan jihar Rivers ya ce ya kamata zaɓen 2027 ya ta’allaka ne kan ƙwarewa da gogewa da kuma abin da mutum ya aikata a baya, ba wai son zuciya, lura da ƙabila ko yanki ba.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Amaechi ya ce:

“Abin da ya kamata ‘yan Najeriya su yi shi ne su tantance dukkanmu da muke neman muƙami bisa tarihin ayyukanmu.
Rt Hon Chibuike R Amaechi
Rotimi Amaechi na hira da 'yan jarida bayan mayar da fom din ADC a Abuja. Hoto: Rt Hon Chibuike R Amaechi
Source: Facebook

Gwamna Zulum ba zai yi takara ba

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sanar da cewa ba zai yi takara ba a zaben 2027.

Farfesa Zulum ya bayyana cewa 'yan uwa da abokan arziki sun matsa masa lamba da cewa ya nemi sanata amma a karshe ya ki yarda da hakan.

Gwamnan jihar Borno ya sanar da haka ne yayin zama da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a Maiduguri gabanin zaben fitar da gwani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng