'Yan Adawa Sun Dimauce da INEC Ta Kawo Amfani da Sojoji a Zaɓen 2027

'Yan Adawa Sun Dimauce da INEC Ta Kawo Amfani da Sojoji a Zaɓen 2027

  • Jam'iyyun adawa a Najeriya sun bayyana rashin amincewa da matakin da hukumar zabe ta kasa, INEC ke shirin dauka game da zaben 2027
  • Hukumar INEC ta sanar da fargaba game da rashin tsaro a yayin zabukan kasar nan, inda ta bayyana aniyarta na amfani da sojoji a 2027
  • Sai dai jam'iyyun adawa suna ganin akwai wata 'kasa, matukar za a yi amfani da jam'an sojin wajen saka ido a kan yadda za a gudanar da zabukan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta bayyana damuwa kan yadda matsalar rashin tsaro ke ƙara tsananta a Najeriya.

Shugaban hukumar Joash Amupitan da ya bayyana haka ya kawo hanyar tabbatar da an gudanar da sahihin zabe ta hanyar amfani da jami'an sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Da sake: Amnesty ta nemi a bi jinin matasan Kano da aka kashe bayan naɗa Garo

Yan adawa sun yi fatali da shirin hukumar INEC
Shugaban INEC Joash Amupitan a lokacin da ya isa majalisa domin a tantance shi a 2025 Hoto: Nigerian Senate
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa jam'iyyun adawa sun bayyana cewa akwai lauje a cikin nadi, inda suka yi gaggawar fatali da duk wani tsari da zai jawo soja cikin zaben.

Yan Najeriya sun yi fatali da shirin INEC

Shugaban ƙungiyar Obidient Movement, Dakta Yunusa Tanko, ya ce aikin kula da tsaron cikin gida ya kamata ya kasance a hannun ‘yan sanda da sauran hukumomin farar hula.

Ya ce gwamnati na iya amfani da matsalar rashin tsaro a matsayin wata hanya ta kawo tsaiko ga zaɓe, musamman ganin yadda ake hasashen cewa Peter Obi zai kasance cikin masu fafatawa.

Shi ma sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar LP Ken Asogwa, ya ce bai dace a riƙa tunanin amfani da sojoji wajen kula da harkokin zaɓe ba.

A cewarsa, aikin zaɓe abu ne na farar hula, don haka jami’an tsaro irin su NSCDC da ‘yan sanda su ne suka kamata su kula da shi.

Kara karanta wannan

NDC ta kashe gobarar da ta taso mata a Kano, an biya bukatar shugaban jam'iyya

'Yan adawa sun dura kan INEC

Jam’iyyar PDP ƙarƙashin kwamitin riƙo na Farfesa Tanimu Turaki ta bayyana cewa rashin nuna adalci a cikin INEC ya fi matsalar rashin tsaro barazana ga sahihin zaɓe.

Sakataren yaɗa labaran kwamitin, Ini Ememobong, ya ce INEC ta fi dacewa ta mayar da hankali wajen tabbatar da gaskiya da adalci maimakon batun tura sojoji.

Yan adawa sun ce yan sanda ne ya kamata su kula da tsaro zabe
Shugaban hukumar zaben Najeriya, Amupitan a aBUJA hOTO: INEC Nigeria
Source: Facebook

Jam’iyyar NNPP ma ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta magance matsalar rashin tsaro kafin lokacin zaɓe mai zuwa.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya ce watanni takwas sun isa gwamnati ta fara samun nasara wajen daƙile matsalar tsaro idan har da gaske take son gudanar da zaɓe cikin lumana.

INEC ta hango matsala ga zaben 2027

A baya mun wallafa cewa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) Farfesa Joash Amupitan, ya nuna damuwa kan bukatar gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa.

Farfesa Amupitan ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro na barazana ga gudanar da sahihin zabe a Najeriya ganin yadda ake fama da tashe-tashen hankula a bangarori daban-daban a Najeriya.

Shugaban hukumar na INEC ya nuna muhimmancin da ke akwai wajen yin hadin gwiwa da hukumomin tsaro domin magance matsalar inda ya bayyana cewa za a iya amfani da sojoji don dakile barazanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng