Kotu Ta Shirya Yanke Hukunci kan Sahihancin Takarar Jonathan a 2027
- Wata kotun tarayya da ke Abuja za ta saurari karar da aka shigar kan abin da ya shafi takarar tsohon shugaban kasa a Najeriya
- Ana korafi ne domin hana Goodluck Jonathan tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 da ake tunkaea a kasar
- Lauyan da ya shigar da karar ya ce Jonathan ya riga ya cika wa’adin mulki biyu bayan kammala zangon Umaru Musa Yar’Adua da kuma cin zaben 2011
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar raba gardama game da korafi kan hana Goodluck Jonathan tsayawa takara.
Wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ne ya ke korafi ka takarar tsohon shugaban kasar inda ya ce ya saba ka'ida.

Source: Facebook
Takarar Jonathan: Kotu za ta raba gardama

Kara karanta wannan
Matasa sun yi cincirindo a gidan Jonathan kan zaben shekarar 2027, sun fadi bukatarsu
Rahoton TheCable ya ce kotun ta sanya ranar 8 ga watan Mayun 2026 domin sauraron karar wanda zai fayyace sahihancin takarar tasa.
Lauya Johnmary Jideobi yana neman kotu ta bayyana cewa Jonathan bai cancanci sake neman kujerar shugaban kasa ba bisa tanadin kundin tsarin mulki.
A ranar 28 ga watan Afrilun 2026, alkalin kotun, Mai Shari’a Peter Lifu, ya bayar da umarnin aika sammaci ga wadanda ake kara bayan sun kasa gabatar da martaninsu.
Jonathan shi ne wanda ake kara na farko a karar mai lamba FHC/ABJ/CS/2102/2025, yayin da aka hada Hukumar INEC da babban lauyan gwamnatin tarayya cikin wadanda ake kara.
Mai karar ya roki kotu ta hana Jonathan gabatar da kansa ga kowace jam’iyya domin neman tikitin takarar shugaban kasa a 2027.
Haka kuma ya bukaci kotu ta hana INEC karba ko wallafa sunan Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Source: Getty Images
Musabbabin kai karar Jonathan kotu
Jideobi ya bayyana cewa Jonathan ya riga ya cika iyakar wa’adin mulkin shugaban kasa bayan ya karbi mulki sakamakon rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua a shekarar 2010.
Daga baya Jonathan ya sake cin zaben shugaban kasa a 2011 kuma ya yi cikakken wa’adi, abin da mai karar ke cewa ya cika sharadin wa’adi biyu da kundin tsarin mulki ya tanada.
A cikin takardar rantsuwar goyon bayan karar, Emmanuel Agida ya ce rade-radin cewa Jonathan na tunanin sake tsayawa takara ne ya sa suka dauki matakin shari’a, cewar Daily Post.
Ya kara da cewa idan aka bar Jonathan ya tsaya takara kuma ya ci zabe, hakan zai sa ya sake rantsuwa a matsayin shugaban kasa karo na uku, wanda zai saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Mai karar ya jaddada cewa an shigar da karar ne domin kare doka, tabbatar da martabar kundin tsarin mulki da kuma kare tsarin dimokuradiyyar Najeriya.
Matasa sun cika gidan Jonathan kan takarar 2027
A wani labarin, kun ji cewa matasan sun yi cincirindo a gidan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan domin takara a zaben 2027.
Matasan sun taru a gidan tsohon shugaban kasar da ke Maitama a Abuja, suna rera wakoki da raye-raye na nuna goyon baya a gare shi.
Sun bukaci Jonathan da ya fito a dama da shi domin shiga takarar shugaban kasa a zaben 2027, suka bayyana shi a matsayin wanda zai iya ceto Najeriya.
Asali: Legit.ng
