Sauki Ya Samu: Gwannatin Tinubu Ta Kaddamar da Motocin CNG da na Lantarki a Kano
- Gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da shirin motocin CNG da na lantarki a Kano domin rage kuɗin sufuri da bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta
- Gwamna Abba Yusuf ya ce shirin zai taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga, rage wahalar man fetur da kare muhalli a jihar Kano
- Hukumar PI-CNG & EV ta bayyana cewa an horar da sama da ‘yan Najeriya 7,000 tare da kafa cibiyoyin gyaran CNG 41 a sassan jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - An ƙaddamar da shirin gwamnatin tarayya na motocin CNG da na lantarki a jihar Kano, wani mataki da ake ganin zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri da bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta a Najeriya.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya ƙaddamar da shirin ranar Alhamis, inda ya ce wannan na daga cikin ƙoƙarin tallafa wa manufofin gwamnatin tarayya na amfani da makamashi na zamani a harkokin sufuri.

Source: Twitter
An kaddamar da motocin CNG a Kano
Gwamnan ya ce gwamnatin Kano za ta ci gaba da samar da ingantaccen tsarin sufuri domin rage wahalar zirga-zirga da kuma rage kuɗin da jama’a ke kashewa wajen sufuri, in ji rahoton Arise News.
Ya kara da cewa shirin zai taimaka wajen kare muhalli da rage dogaro da man fetur da ake amfani da shi wajen tafiyar da ababen hawa.
Da yake jawabi a wajen taron, mai kula da shirin CNG na kasa, Barista Isma’il Ahmad, ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin sauya tsarin sufuri a Najeriya.
Ya ce gwamnatin Tinubu tana son samar da hanyoyin sufuri masu sauki da kuma amfani da makamashi mai tsafta domin rage radadin cire tallafin man fetur.
An kafa cibiyoyin gyaran CNG a Kano
Isma’il Ahmad ya bayyana cewa tun bayan fara shirin, hukumar PI-CNG & EV ta yi aiki tare da gwamnatocin jihohi, kamfanoni masu zaman kansu, cibiyoyin kuɗi da masu harkar sufuri domin bunƙasa tsarin amfani da gas wajen sufuri a Najeriya.

Kara karanta wannan
An saki sunayen kananan hukumomi 3 da Boko Haram ta tilasta wa biyan haraji a Yobe
Ya ce kawo yanzu an fara aiwatar da shirin gyaran motocin CNG a jihohi sama da 28 a Najeriya.
A cewarsa, an kuma samar da tashoshin sayar da gas sama da 58 tare da tura dubban bas-bas da adaidaita sahu masu amfani da CNG a manyan hanyoyin sufuri.
Ya kara da cewa Kano na da cibiyoyin gyaran motocin CNG guda 41 daga cikin sama da cibiyoyi 300 da aka kafa a Najeriya, in ji rahoton Punch.

Source: Twitter
An horar da matasa 7,000 kan harkokin CNG
Jami’in ya bayyana cewa sama da matasan Najeriya 7,000 aka horar kan harkokin CNG da motocin lantarki domin samar da ayyukan yi da bunkasa fasahar zamani a fannin sufuri.
Ya ce shirin zai taimaka wajen samar da sabbin damammaki ga matasa tare da rage tsadar sufuri da dogaro da man fetur.
Masu lura da al’amura sun bayyana cewa shirin motocin CNG da lantarki na iya taimakawa wajen rage tsadar rayuwa idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata.
Matakan da Tinubu ya dauka kan CNG

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta sa baki kan harin sojojin sama da ya kashe farar hula a Zamfara
A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartarwa na kwanaki biyu, inda majalisar ta amince da ayyuka da tsare-tsare 20.
A cikin wadannan ayyuka da tsare-tsaren, akwai wadanda kacokan suka fito da kudurorin Tinubu na janye Najeriya daga dogara da fetur zuwa iskar gas.
Matakin farko da Tinubu ya dauka shi ne ba da umarnin cewa ma’aikatu da hukumomin gwamnati su koma sayo ababen hawa da ke amfani da iskar gas din CNG.
Asali: Legit.ng
