Jonathan Ya ba Ƴan Najeriya Amsa kan Kiran Tsayawa Takara a Zaɓe a 2027

Jonathan Ya ba Ƴan Najeriya Amsa kan Kiran Tsayawa Takara a Zaɓe a 2027

  • Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi magana game da yiwuwar tsayawa takara a zaben shekarar 2027
  • Jonathan ya yi karin haske ne yayin da matasa masu bukatar ya tsaya takarar shugaban kasa suka kai masa ziyara
  • Tsohon shugaban ya bukaci matasan Najeriya su ci gaba da neman sahihin zabe na gaskiya, yana mai cewa dimokuradiyya tana bunkasa ne idan jama'a sun taka rawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wasu matasa sun ziyarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan domin neman ya tsaya takara a zaben 2027.

Goodluck Jonathan ya yi magana kan kiraye-kirayen da matasan Najeriya ke yi masa game da takarar shugaban kasa tun bayan barin mulki.

An taso Jonathan a gaba ya yi takara
Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Goodluck Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Facebook

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da kungiyar matasa a ofishinsa da ke Abuja, cewar Arise TV.

Kara karanta wannan

Matasa sun yi cincirindo a gidan Jonathan kan zaben shekarar 2027, sun fadi bukatarsu

Jonathan ya magantu kan takara a 2027

Jonathan ya ce ya fahimci bukatun da matasan suka gabatar masa, amma bai bayyana aniyarsa ta shiga takarar shugaban kasa ba.

Ya ce zai tuntubi mutane da dama tare da yin nazari sosai kafin daukar matakin da ya dace kan tsayawa takara.

“Ina jin ku sosai kuma na fahimci sakonnin da kuka kawo. Zan tuntubi mutane daban-daban kafin yanke duk wata muhimmiyar shawara."

- In ji Jonathan

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi kira ga matasa su kara shiga harkokin siyasa tare da kare sahihin zabe da dimokuradiyya a Najeriya.

Ya ce dimokuradiyya ba za ta bunkasa ba idan jama'a suka zabi zama masu kallo kawai, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Jonathan ya gano matsalolin Najeriya kan takara
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan yayin taro a Abuja. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Twitter

Matsalolin da Jonathan ya hango a Najeriya

Jonathan ya nuna damuwa kan yadda mutane da dama ba sa fitowa zabe a Najeriya, inda ya bayyana cewa rashin sha'awar kada kuri'a yana daga cikin manyan matsalolin dimokuradiyya da kasar ke fuskanta a yanzu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya umarci tsohon gwamna, Ayade ya hakura da neman takara a 2027

Ya ce Najeriya na daga cikin kasashen da yake gani da yawan masu kin shiga zabe idan aka kwatanta da sauran zabukan da ya taba lura da su a duniya.

Jonathan ya bukaci matasa su kasance masu ruwa da tsaki wajen harkokin siyasa, gudanar da zabe, da kuma sauran ayyukan cigaban kasa.

Ya ce matasa suna da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingantacciyar dimokuradiyya.

Tsohon shugaban kasar, wanda ya jagoranci Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015, na cikin fitattun ‘yan siyasar da ake yawan ambata yayin tattaunawar siyasar zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Matasa na neman Jonathan ya yi takara

A baya, an ji cewa wasu matasa sun yi wa gidan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a Abuja dafifi a kan batun neman ya tsaya takara a zaben 2027.

Masu zanga-zangar sun ce sun yi shawarwari a fadin ƙasa kafin neman Jonathan ya dawo kujerarsa wanda ya sauka a shekarar 2015 bayan faduwa zaɓe.

Jonathan bai gana da matasan ba, amma ana ci gaba da matsa masa lamba ya dawo siyasa a dama da shi a zaɓen 2027 domin dawo da martabar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.