2027: Nyesom Wike Ya Magantu kan Tsayar da Dan Takarar Gwamnan Rivers

2027: Nyesom Wike Ya Magantu kan Tsayar da Dan Takarar Gwamnan Rivers

  • Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi karin haske game da batun fitar da dan takara ko goyon bayansa a jihar Rivers
  • Wike ya ce bai goyi bayan kowa domin takarar gwamnan Rivers ta 2027 ba, yana jiran hadakar PDP da APC ta yanke matsaya
  • Ya bayyana cewa ba su aiki tare da Gwamna Siminalayi Fubara, har yana zarginsa da karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa bai amince da wani mutum domin takarar gwamnan Rivers ta shekarar 2027 ba.

Tsohon gwamnan Rivers ya ce sai hadakar jam'iyyun PDP da APC ta gana kafin daukar irin wannan matsaya da ke da matukar muhimmanci.

Wike ya ƙaryata tsayar da dan takarar gwamna a Rivers
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara. Hoto: Nyesom Wike, Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Wike ya yi wannan bayani ne yayin tattaunawar manema labarai a Abuja ranar Laraba 6 ga watan Mayun 2026, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Kano: Gawuna ya bi sahun Kwankwaso, ya bayyana dalilinsa na barin ADC

Yadda rikicin siyasar Rivers ta barke

Hakan ya biyo bayan rikicin siyasa da ta barke musamman tsakanin Gwamna Fubara da tsohon mai gidansa, Nyesom Wike.

An dade ana fama da rikicin siyasa tsakanin Wike da Fubara tun bayan zaben 2023, duk da cewa Wike ne ya marawa Fubara baya domin ya gaje shi.

A cewar Wike, shugaban kasa ya shiga tsakani domin samar da zaman lafiya lokacin rikicin tsige Fubara.

Ya ce daga baya gwamnan ya sauya matsaya bayan an janye yunkurin tsige shi da aka yi a wancan lokaci a Rivers.

Rawar da Bola Tinubu ya taka wajen sulhu

Rikicin ya kara kamari lokacin da ‘yan majalisar da ke goyon bayan Wike karkashin Rt. Hon. Martin Amaewhule suka fara kokarin tsige Fubara daga kujerarsa ta gwamna.

Wannan rikici ya sa Shugaba Tinubu ya dakatar da Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu da ‘yan majalisar Rivers a watan Maris na shekarar 2025 saboda rikicin siyasar.

Kara karanta wannan

Ficewar Obi, Kwankwaso ya jawo farraka a gefen adawa kan tsayar da dan takara 1

Bayan watanni shida, Tinubu ya dage dokar ta-baci tare da dawo da Fubara, mataimakiyarsa da ‘yan majalisar bayan wata sulhu da aka gudanar tsakanin bangarorin rikicin.

Sulhun ya biyo bayan ganawar da Tinubu ya yi da Wike, Fubara, Amaewhule da sauran ‘yan majalisar Rivers, inda aka samu matsaya domin kawo karshen rikicin siyasar jihar.

Wike ya sake caccakar Fubara
Tsohon gwamnan Rivers kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike. Hoto: Nyesom Wike.
Source: Twitter

Alakar da ke tsakanin Wike da Fubara

Wike ya ce suna da magoya baya a PDP da APC inda ya bayyana hadakar a matsayin dabarar siyasa, kamar yadda TheCable ta ce.

Tsohon gwamnan Rivers ya kuma ce ba sa aiki tare da Gwamna Siminalayi Fubara, wanda ake rade-radin yana neman tikitin APC domin zaben gwamna mai zuwa a jihar.

Ya zargi Fubara da karya yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsa da ‘yan majalisar Rivers a gaban Shugaba Bola Tinubu, yarjejeniyar da ta hana tsige gwamnan.

Rikicin PDP: Wike ya magantu bayan hukuncin kotu

Mun ba ku labarin cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi martani bayan Kotun Koli ta yi hukunci game da rikicin shugabancin PDP da ADC.

Kara karanta wannan

Pantami zai yi yaki da zalunci wajen fitar da dan takarar gwamnan APC a Gombe

Wike ya ce hukuncin Kotun Koli ya kawo ƙarshen rikicin cikin PDP, yana tabbatar da cewa jam’iyyar yanzu tana da shugabanci guda ɗaya kacal.

Tsohon sanatan ya nanata cewa taron Ibadan da ya samar da shugabancin Tanimu Turaki ya sabawa umarnin kotu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.