Farashin Wake, Doya da Sauran Kayan Abinci Ya Haura Sama a Kano da Wasu Jihohi
- Hukumar NBS ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ta ƙaru zuwa 15.69% a watan Afrilun 2026 daga 15.38% da aka samu a Maris
- Jihohin Sokoto, Bauchi da Zamfara ne suka fi fama da tashin farashi, yayin da Edo, Borno da Jigawa suka samu mafi ƙarancin hauhawar farashi
- Farashin kayan abinci ya ragu idan aka kwatanta da bara, yayin da farashin gero, doya, tumatur da wake suka taka rawa wajen samar da sauyin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ta ƙaru zuwa 15.69% a watan Afrilun shekarar 2026.
Rahoton hukumar ya nuna cewa wannan mizanin kiddiddigar ya fi na watan Maris wanda ya tsaya a 15.38%, lamarin da ke nuna karin 0.31%.

Source: Getty Images
Sauyin farashin kayayyaki a watan Afrilu
Sai dai hukumar ta ce duk da karin da aka samu, sabon wannan alkaluman sun yi ƙasa idan aka kwatanta da 26.82% da aka samu a watan Afrilun shekarar 2025, in ji rahoton Daily Trust.
A cewar rahoton NBS, idan aka duba daga wata zuwa wata, hauhawar farashin watan Afrilu ta tsaya a 2.13%. Hakan ya nuna raguwar 2.05% idan aka kwatanta da watan Maris wanda aka samu 4.18%.
Hukumar ta ce hakan na nufin yadda farashin kaya ke ƙaruwa a watan Afrilu ya ragu idan aka kwatanta da yadda ya kasance a watan Maris.
Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta kai 16.06% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
An samu sauyin farashin kayan abinci
NBS ta ce an samu karin farashi kadan a kan farashin kayayyakin abinci irin su gero, garin doya, citta, naman sa, garin rogo, doya, barkono, kifi busasshe, rogo, wake, dankalin turawa, tumatur, alkama, waken soya, dawa da ayaba.
Hukumar ta kuma bayyana cewa matsakaicin hauhawar farashin kayan abinci na watanni 12 zuwa Afrilun 2026 ya tsaya a 17.55%.
Wannan ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da 34.60% da aka samu a shekarar 2025, in ji rahoton Vanguard.
Jihohin da suka fi fama da tsadar rayuwa
Rahoton ya nuna cewa jihohin Sokoto, Bauchi da Zamfara ne suka fi fama da hauhawar farashi idan aka duba daga shekara zuwa shekara.
Sokoto ce ta zo ta farko da 25.74%, sai Bauchi da 22.52%, yayin da Zamfara ta samu 22.03%.A gefe guda kuma, jihohin Edo, Borno da Jigawa ne suka samu mafi ƙarancin tashin farashi.

Source: Getty Images
Idan aka duba daga wata zuwa wata, jihohin Neja, Kano da Filato ne suka fi samun karin farashi a watan Afrilu.
Neja ta samu 5.66%, Kano 4.50%, yayin da Filato ta samu 4.39%. Sai dai Bayelsa, Enugu da Rivers sun samu raguwar hauhawar farashi a wannan lokaci.
A bangaren kayan abinci kuwa, jihar Enugu ce ta fi fama da tsadar kayan abinci da 32.67%, sai Kwara da 30.77% da Adamawa da 30.14%.
An samu karuwar farashin abinci
A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar NBS ta fitar da rahoto game da farashin kayayyaki a watan Maris na shekarar 2026, inda ta nuna karuwar farashi.
A bayanin da ta yi, cibiyar NBS ta bayyana wasu nau'ukan kayan abinci da tashin farashinsu ya jawo karuwar tsadar kayayyaki a Najeriya.
Hukumar NBS ta ambaci wasu jihohi da suka hada da Zamfara, Sokoto, Bauchi da sauransu da ta ce sun fi fuskantar matsalar hauhawar farashin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


