Obika: Dalilin da Ya Sa Dan Majalisar Tarayya Ya Canza Jam'iyya Sau 2 cikin Watanni 2
- Dan Majalisar wakilai, Hon. Joshua Chinedu Obika ya kare kansa game da matakin da ya dauka na sauya jam'iyyu biyu cikin kankanin lokaci
- Hon. Obika ya koma APC mai mulki a watan Maris, kuma a farkon wannan wata na Mayu da muke ciki, ya sake sauya sheka zuwa NDC
- 'Dan majalisar ya ce wani lokaci ‘yan siyasa na bukatar sauya jam’iyya domin ci gaba da kasancewa masu tasiri a siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Abuja Municipal/Bwari, Hon. Joshua Chinedu Obika, ya kare matakin sauya jam’iyyu biyu cikin watanni kadan.
Ya ce shawarar tasa ta samo asali ne daga yanayin siyasa da kuma biyayya ga tafiyar “sabuwar Najeriya” da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ke jagoranta.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya hakura, ya shirya goyon bayan Peter Obi ko wani 'dan takara a zaben 2027

Source: Facebook
Obika ya fice daga jam’iyyar LP zuwa APC mai mulki a watan Maris, sannan ya koma jam’iyyar NDC a farkon wannan watan na Mayu, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Yayin da yake zantawa da ‘yan jarida kan sukar da ake masa saboda yawan sauya jam’iyya cikin kankanin lokaci, ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su fi mayar da hankali kan ayyukan shugabanni maimakon jam’iyyar da suke ciki.
Dan majalisa ya fadi dalilin barin LP
Obika ya ce rikicin cikin gida da ya dabaibaye LP ya raunana tsarin jam’iyyar tare da rage ingancinta, yana mai misali da yadda Hukumar Zabe (INEC) ta kasa sanya sunayen ‘yan takararta a lokacin zaben kananan hukumomin Abuja.
Ya bayyana cewa tun farko bai son barin LP saboda biyayyarsa ga Peter Obi, wanda ya bayyana a matsayin jagoransa na siyasa, yana mai cewa sai da ya tabbatar tsohon gwamnan ya hade kai da ADC sannan ya fara tunanin ficewa.
Sai dai Obika ya ce yana da shakku kan tsarin ADC a lokacin, yana zargin cewa da dama daga cikin wadanda suka kafa kawancen abokan siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ne.
Ya ci gaba da cewa Peter Obi da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, su ne ‘yan siyasar da suke da mafi karfin goyon bayan jama’a kai tsaye wajen kawo sauyi a kasa, yana mai cewa dole ne su hada kai domin cigaban Najeriya.

Source: Facebook
Dalilin yawan canza jam'iyyar Hon. Obika
Dan Majalisar ya ce ya shiga APC na dan lokaci ne saboda jam’iyyar tana da kwanciyar hankali yayin da rikicin LP ke kara kamari, amma daga baya ya koma NDC bayan Obi ya shiga cikinta.
Da yake kare sauya jam’iyyunsa akai-akai, dan majalisar ya ce wani lokaci ‘yan siyasa na bukatar sauya jam’iyya domin ci gaba da kasancewa masu tasiri a siyasa da kuma cimma manufofinsu.
“Peter Obi da kansa ya sauya jam’iyyu da dama. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ma haka. Muhimmin abu shi ne gano mutanen da suka kuduri aniyar inganta kasar nan,” in ji shi.
Yan Majalisar wakilai 17 sun koma NDC
A wani labarin, kun ji cewa aƙalla 'yan majalisar wakilai 17 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar ADC zuwa NDC, a wani mataki da ke ƙara sauya fasalin siyasar Najeriya.
An bayyana sauyin sheƙar ne a hukumance a zauren majalisar wakilai yayin zaman ranar Talata, 5 ga watan Mayu, 2026.
Daga cikin ‘yan majalisar da suka sauya sheka zuwa NDC akwai Yusuf Datti , Uchenna Okonkwo, Adamu Wakili,da Thaddeus Attah.
Asali: Legit.ng

