Bello El Fufai Ya Fice daga Jam'iyyar APC Mai Mulki, Ya Sake Fitowa Takara a Zaben 2027

Bello El Fufai Ya Fice daga Jam'iyyar APC Mai Mulki, Ya Sake Fitowa Takara a Zaben 2027

  • 'Dan Majalisar wakilai daga jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya sauya sheka daga APC mai mulki zuwa jam'iyyar hadaka ta ADC
  • Bello, 'dan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ayyana shirinsa na sake neman kujerar Majalisar wakilai a Kaduna ta Arewa a 2027
  • Ya kuma tabbatarwa al'ummar mazabarsa cewa duk da wannan sauyi da aka samu, ayyukan da ya dauko zai su ci gaba kamar yadda aka tsara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Bello El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa ADC a hukumance.

Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ne ya karanta wasiƙar sauya shekar Bello El-Rufai a zaman majalisar na ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu, 2027.

Bello El-Rufai.
Dan Majalisar Kaduna ta Arewa, Hon. Bello El-Rufai a zaman Majalisar wakilai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

'Dan El-Fufai ya fice daga jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

Ganduje, Shekarau sun raka Garo shiga ofishin mataimakin gwamnan Kano

Bello El-Fufai, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa a Majalisar wakilai ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Tajudeen Abbas ya ce Bello El-Rufai ya shiga ADC tare da wasu ‘yan majalisar biyu na jam’iyyar PDP daga jihar Kaduna, Hon. Umar Ajilo da Hon. Suleiman Yahaya Richifa.

Bello El-Rufai ya tabbatar da cewa zai sake neman takarar kujerar Majalisar wakilai a mazabar Kaduna ta Arewa karkashin inuwar jam'iyyar ADC a zaben 2026.

Bello El-Rufai zai sake neman takara a 2027

A sanarwar da ya fitar, Bello ya ce:

"Sa’o’i kadan da suka gabata, Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon Tajudeen Abbas (GCON), ya karanta wasikar ficewa ta daga APC da kuma komawa ta ADC a hukumance.
"A yanzu ni mamba ne a jam’iyyar ADC, kuma zan nemi sake tsayawa takara domin ci gaba da wakiltar mutanen kirki na mazabar Kaduna ta Arewa a karkashin wannan jam’iyya."

'Yan Majalisa 2 sun bi Bello zuwa ADC

Ya kara da cewa ya koma ADC ne tare da Hon. Suleiman Richifa, mai wakiltar Soba, da kuma Hon. Umar Ajilo, mai wakiltar Makarfi/Kudan.

Kara karanta wannan

NDC ta kara karfi a majalisa, sanatan ADC ya sauya sheka zuwa sabuwar jam'iyyar

'Dan tsohon gwamnan ya tabbatar wa mutanen mazabafsa cewa zai ci gaba da ayyukansa yadda ya kamata ba tare da gajiya ba domin sauke amanar da suka dora masa.

Majalisar wakilai.
Zauren Majalisar wakilai yayin da ake tsakiyar zama a Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Bello ya ce nan ba da dadewa ba zai sanar da kwamitin wucin gadi na shirin inganta cibiyoyin kiwon lafiya da ya kaddamar a makon jiya.

"Za mu samar magunguna da kayan aiki ga asibitocin mu na kiwon lafiya, inda za mu fara da raba sirinji guda 1,000 ga kowane asibiti da sauran muhimman kayayyaki.
"Kashi na farko zai fara ne da cibiyoyi guda biyu: mazabar Unguwar Sarki da mazabar Badarawa/Malali," in ji Bello El-Rufai.

Yan Majalisa 17 sun bar ADC zuwa NDC

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan majalisar wakilai 17 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar ADC zuwa NDC bayan shigar Kwankwaso da Peter Obi.

Daga cikin ‘yan majalisar da suka sauya sheka zuwa NDC akwai Yusuf Datti, Uchenna Okonkwo, Adamu Wakili, Thaddeus Attah, George Ozodinobi, Lilian Orogbu, Oluwaseyi Sowunmi, da Peter Aniekwe.

Sun bayyana sauyin sheƙar ne a hukumance a zauren majalisar wakilai yayin zaman ranar Talata, 5 ga watan Mayu, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262