Amaechi Ya Mika Fom din Neman Takara a ADC, Ya Fadi a Lokacin da Zai Gyara Najeriya
- Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya mika fom dinsa na neman takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar ADC
- Rotimi Amaechi ya bayyana lokacin da zai kwashe wajen gyara Najeriya idan har aka ba shi dama a zaben shekarar 2027
- Hakazalika, tsohon Ministan ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi cancanta daga cikin masu neman darewa kan madafun ikon kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Ministan sufuri kuma mai neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya yi alkawarin gyara Najeriya.
Rotimi Amaechi ya yi alƙawarin sauya fasalin Najeriya cikin shekaru huɗu idan aka zaɓe shi a babban zaɓen 2027.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa Amaechi ya yi wannan alƙawarin ne jim kaɗan bayan miƙa takardunsa na tsayawa takara a babban sakatariyar jam’iyyar ADC ta ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Ministan Tinubu da ya yi murabus ya ayyana shiga takarar gwamna a Oyo
Amaechi ya kuma ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tare da ɗora mata alhakin taɓarɓarewar tattalin arziƙi da ake fama da shi a ƙasar.
Me Amaechi ya ce kan zaben 2027?
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce ya kamata zaɓen 2027 ya ginu ne bisa cancanta, ƙwarewa, da kuma bajinta maimakon ra’ayin ƙabila ko na yanki, jaridar TheCable ta kawo labarin.
“Abin da ya kamata ’yan Najeriya su yi shi ne su tantance dukkanmu masu neman takara bisa ga ayyukanmu na baya."
“Kusan kowa da ke takarar shugaban ƙasa ya yi wa Najeriya hidima ta wata hanya. Bari wannan zaɓen ya zama kamar jarrabawa. Idan ka nuna bajinta, duk wanda ya fi ɗayan bajinta, to a zaɓi wannan mutumin.”
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya yabi kansa
Amaechi ya bayyana cewa shekarunsa a kan muƙaman gwamnati sun shirya shi don aikin jagorantar ƙasar, inda ya buga misali da lokacin da yake gwamna sannan daga baya ya zama Ministan sufuri a ƙarƙashin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
“Abu na gaba shi ne, wane ne ke da ikon samun ƙuri’u? Wane ne ke da ikon doke mai ci a yanzu? Wane ne yake da ƙwarewa? Na yi amanna cewa ni ne na fi kowa ƙwarewa.”
“Ina da sauran ƙuruciya, ni ne na fi kowa ƙwarewa, kuma na yi amanna cewa ina da iko. Ku koma jihar Rivers ku ga abin da na yi. Ku koma ma’aikatar sufuri ku ga abin da na yi, sannan ku tantance ko zan iya sauya fasalin ƙasar nan. Kuma zan sauya ƙasar nan cikin shekaru huɗu."
- Rotimi Amaechi

Source: Twitter
Amaechi wanda ya yi gwamnan jihar Rivers daga 2007 zuwa 2015, ya kasance babban jigo wajen kafa jam’iyyar APC, sannan daga baya ya yi aiki a matsayin shuganan kwamitin yaƙin neman zaɓen marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a 2015.
Amaechi ya kalubalanci Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu kan zaben 2027.
Rotimi Amaechi ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu da ya bari a gudanar da sahihin zabe a shekarar 2027 da ke tafe.
Amaechi ya bayyana cewa ’yan Najeriya da dama suna ɗokin ganin sun kori Shugaba Bola Tinubu daga kan mulki a zaɓen shekarar mai zuwa.
Asali: Legit.ng
